‘Yan bindigar da su ka yi wa fadar Basaraken Oso-Ajowa Akoko dirar mikiya a gida su ka arce da shi, sun nemi lallai a biya fansar naira miliyan 100 sannan a sake shi.
An dai yi garkuwa da Basarake Clement Jimoh a ranar Alhamis, yayin da wasu dandazon ‘yan bindiga su ka kewaye fadar sa a jihar Ondo, su ka riƙa buɗe wuta.
Sun firgita mutane da harbe-harben da su ka riƙa yi, sannan daga baya su ka afka cikin gidan, su ka yi awon-gaba da shi.
Majiya daga iyalan basaraken ta shaida wa wakilin mu cewa a ranar Juma’a ‘yan bindigar sun kira iyalan sa ta waya, su ka nemi sai an biya naira miliyan 100 sannan za su sake shi.
Har zuwa yanzu dai ‘yan sakai da ke masarautar na can sun bazama a cikin jeji neman inda za su yi arangama da ‘yan bindigar, domin su ceto sarkin su.
Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami ta shaida wa wakilin mu cewa jami’an su na bakin ƙoƙarin ganin sun ceto basaraken.
Al’ummar garin kuwa tuni su ka fara addu’o’i da azumi da tsayuwar-dare, domin addu’o’in kuɓutar basaraken na su.
Sai dai kuma Kakakin ‘Yan Sanda ta ce ba su da masaniyar masu garkuwar sun nemi a biya su naira milyan 100 kuɗin fansar basaraken.
Discussion about this post