Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku/Okowa ta bugi gaban cewa jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar ne za su lashe zaɓen 2023, tun da jijjifin safiya.
Kakakin Yaɗa Labaran Yaƙin Neman Zaɓen Atiku/Okowa, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata, a Abuja.
Ologbondiyan ya ƙara da cewa irin yadda Atiku Abubakar ke samun ɗimbin masoya ya nuna cewa hakan babbar alama ce mai nuni da cewa tun kafin a yi nisa da fara jefa ƙuri’a Atiku zai lashe zaɓen 2023, a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
“Kun ga dai Atiku ya samu goyon bayan kusan mafi yawan ‘yan Najeriya, waɗanda ma ba su cikin rukunin da masu yin ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ke lissafawa da su a kintacen wanda zai yi nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
“Tun da jijjifin safiya Atiku zai lashe yawancin ƙuri’un da aka kaɗa, kuma nan da nan zai samu kashi 25 bisa 100 na aƙalla jihohi 24 a faɗin ƙasar nan.”
Ya nuna cewa jama’a sun gaji da mulkin APC, wanda su ka ɗanɗana tsawon shekaru takwas amma ba su ji daɗin komai ba.
Ologbondiyan ya ce a fili ta ke babu wani ɗan takarar da ya kai Atiku cancanta, kuma babu wanda ya kai shi samun karɓuwa a dukkan faɗin ƙasar nan. Saboda haka a wurin zaɓe tun da sanyin safiya zai yi wa sauran ‘yan takarar fintinkau.
Sai dai kuma Ologbondiyan bai ce komai ba dangane da naƙasun gwamnoni biyar da PDP da Atiku ke fuskanta, waɗanda har yanzu ba su goyi bayan takarar sa ba.