Wani abin mamaki da wannan zamani shine yadda mata da suka Isa suna dakunan mazajensu ke zaune ba tare da sun yi aure ba.
Idan ka tambaye mata irin haka dalilin da ya sa ba su yi aure ba sai su ce maka ra’ayin su ne kawai, ko Kuma su ce lokacin auren ne bai yi ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu mata domin samun wasu dalilai da ke hadda sa haka inda suka yi karin haske kan dalilin da yasa suke zaman kansu batare da aure ba.
1. Talauci da rashin Mazan Aure:
Tallauci na iya hana mace aure. Da yawa sun shaida cewa rashin abin hannu na sa mace ta ji kawai bari ta yi zaman ta kawai ta more rayuwarta iya karfinta. Ko da yake wasu na son yin auren rashin maza ne. ” Mazan aure na matukar wuya. Ba wai babu mazan bane, wanda suke son yin auren nen babu. Maza ba su da kudi, mata kuma kwadayi yayi mana yawa. Dalilin haka tun wadanda suke sonki saboda Allah sun zo, ba za ki yarda da su ba saboda kila ba su kai iya burinki ba, daganan tuna ana budurwa har a tsofe. Shike nan kuma sai mace ta ga za ta iya zama ita kadai ba tare da namiji ba.
2. Sakacin Iyaye
Iyaye a lokutta da yawa na zama ummul abaisan zama matsalar rashin auren mace. Su kan su idan masu kwadayi ne da sanin ya kamata, ba za su maida hankali ba wajen ganin yar su ta yi aure a cikin lokaci, sai lokaci ya kure ana ta neman mai abin hannu.
3. Tsoro
Wasu kuma matan tsoron auren suke yi. ” da yawa daga cikin mata suna tsoron aure. Ba su tunanin ganin kansu karkashin wani namiji suna Bauta masa na aure. Wasu kuma tsoron ma zuwa ne idan suka ga yadda wasu suke a nasu gidajen aure. Sai su rika ganin idan suka yi aure suma haka za su rika fama da zaman aure.
4. Kawaye
Idan mace ba ta yi sa’an kawaye ba, shi kenen ta dulmiya kenan. Wasu bin lalatattun kawaye ne ke saka su cikin wannan hali. ” Kawaye na daga cikin wadanda ke hana mata aure. Idan mace ta na kawaye lalatatta, shikenan sai ta saka ta cikin halin banza. Dagan shikenan anu ya lalace.
5. Son Duniya da Kwadayi
Wasu kuma rudin duniya ce kawai ke dulmiyar da su, da kuma ‘yan cin mata da ake ta cusa wa mata a zukata. Mace sai taga babu wanda ya isa ya saka ta ko kuma ya hana ta. Yadda ta ke so haka za ta rika yi. Wannan na daga cikin abubuwan dake kesa wasu matan su ce ba za su yi auren ba.
Wani shugaban Al’umma da ya tattauna da PREMIUM TIMES, ya yi kira ga iyaye su rika sa wa ya’yan su musamman mata Ido da kuma basu tarbiya ta gari a lokacin da suke yan kanana. Sannan kuma su sanar da su Allah da hukunce hukuncen rayuwa bisa addini.
Discussion about this post