Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a tsawan mulkin sa ya yi kokarin ganin Najeriya ta zama abar gwaji ga wasu kasashe da kuma gyara kasa, amma har yanzu wasu sun saka shi a gama sun tsangwamar sa
Shugaba Bubari ya faɗi haka a wurin taron bikin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Shugaba Buhari ya cika shekaru 80 daidaia a duniya a cikin wannan mako.
” Na yi imani ina iya bakin kokarina amma duk da haka, iyawata ba ta isa ba, wasu ƴan Najeriya na tsangwamata.
” Na ƙosa wa’adin mulki na ya xika in koma gida can Daura in maida hankali kan gonata ka-in-da-na-in. Amma kafin wannan lokacin zan ci gaba da aiki tukuru a matsayina na shugaban kasa domin tabbatar an samu ci gaba mai ɗorewa kamar yadda muka sa a gaba
Mutanen Najeriya na gani a wannan ƙarnin ba a taɓa shugaban kasa da ya samu irin goyon bayan da ƴan Najeriya suka bashi ba kamar shugaba Muhammadu Buhari.
Buhari ya kafa tarihin kada shugaban kasa mai ci a 2015. Sai dai kuma musamman a zangon sa ta biyu, mutanen Najeriya da dama na ganin ba abinda suke tunanin Buhari zai yi wa ƴan Najeriya ne ya ke yi ba.
Misalai da masu hasashe sukan yi kan haɗa da irin matsalolin rashin tsaro da ya addabi musamman yankin Arewa da kuma tsadar kayan abinci da masarufi.
Sannan kuma ga matsalolin tashin man fetur da tsadar rayuwa wanda kafin ya zu an yi tunanin Buhari zai kaeo karshen ireiren wadannan matsaloli ne.
Discussion about this post