Ni dai ba a taba cin watandar N-Power ko kuma N- koma menene ba dani amma irin abinda na ke ji daga waɗanda ke cikin shirin sam babu daɗi. Da yawa daga cikin wadanda suke amfana da wannan shiri a baya sun dai na amfana, abin dai ya zama kamar yaudara ce yanzu ko kuma sun riga sun ci rabon su.
Akwai waɗanda sun shafe watanni sama da biyar ba su samu alawus din su ba, wasu ko ma tunda aka jiƙa su sau ɗaya a shirin ba su sake samun wani abu ba.
Abin da zai tada maka hankali shine, a kullum zaka ga shugabar wannan shiri, Sadiya Farouq ta na ko kaddamar da sabon shirin baiwa marasa karfi tallafi ko kuma agajin gaggawa ga wadanda ibtila’i ya auka ma, amma kuma ga dubbai dake cikin tsarin shirin da aka san shi ba a biyan su hakkunansu da aka yi musu alkawari.
A kwai wata da ta ce min wai ai abinda ya sa ba a biyan su alawus yanzu wai saboda mawaƙi Dbanj ne ya sace kuɗin tas shi ya da duk kasa aka daina biyan alawus ɗin. Abin ya bani mamaki matuka duk da cewa wanda ke faɗin haka ba jahila bace ta san abinda take yi sosai.
Irin wannan fassara da ake yi ba za ka ga laifin su ba, tsananin saka rai ne da jira ya kan sa koma menene aka ce maka game da abin za ka yarda dashi.
Ita gwamnati da Sadiya, shugabar wannan ma’aikata da ke kula da N-Power da saurar shirye-shirye na tallafi da gwamnatin Najeriya ta kirkiro ba su fito ta shaida wa mutane cewa ga abinda ake ciki ba da kuma ga ranar da za a biya waɗanda nasu alawus din ya maƙale ba. Ni a matsayi na na ƴar Najeriya wacce kuma take naam da shiri irin wannan banga dalilin da zai sa idan ba a biya masu karban alawus ba, sai kawai a yi musu shiru tsit su yi ta bankauran su, suna faɗin maganganun gaskiya da karya.
A na wa ganin minista Sadiya ta fito ta fayyace wa masu amfana da wannan shiri halin da ake ciki, idan an daina ne, mutane su sani, idan babu kuɗi ne a sani idan ma yanzu abin ya zama yaudara ce ma’aikatar jinkai ta fito ta sanar wa mutane su sani maimakon abarsu haka kawai shiru, sai hasashen karya da na gaskiya kawai suke yi.
Allah ya basu ikon warware wannan bashi da ke kansu, Amin.
Discussion about this post