Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta iya cika alƙawarin aiwatar da aikin sake gina titin jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Kaduna ba, kamar yadda ta yi alkawarin yi kafin saukar ta.
Ministan Harkokin Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa.
Ya ce babban dalilin kasa cika alƙawarin, shi ne an rasa ƙasar da za a je a ciwo bashin da za a yi ayyukan, amma an rasa.
Cikin watan Maris, ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin titin jirgin, wanda zai keta ta cikin jihohi 14 tsakanin Fatakwal har zuwa Maiduguri.
“Idan an kammala wannan titi zai samar da hanyar kasuwancin bunƙasa tattalin arziki, tare da maida hankali wajen ɗaukar dakon manyan kwantononi daga bakin ruwa, saboda titin sai ya dangane da ruwan Tsibirin Bonny, a Fatakwal,” Inji Buhari.
A lokacin ƙaddamar da aikin, Ameachi ya ce za a kammala shi kafin ƙarshen wa’adin mulkin Buhari a ranar 29 Ga Mayu.
Asalin titin jirgin wanda ya lalace dai Turawan Mulkin Mallaka su ka gina shi tun cikin 1960.
To sai dai kuma wanda ya gaji Amaechi, wato Minista Mu’azu Sambo, ya ce gaskiya a ma daina mafarkin kammala aikin domin babu kuɗin da ma za a ci gaba da aikin ɗungurugum.
“Idan dai ana cewa alƙawari ne wannan gwamnatin ta yi, to maganar gaskiya ba za a iya ma ci gaba da aikin ba kwata-kwata.
“Lokacin da aka ƙaddamar da aikin, an tsara cewa kashi 15 cikin 100 na kuɗaɗen ne kaɗai gwamnatin tarayya za ta iya sanarwa, sauran kashi 85 bisa 100 kuma bashi ne aka yi niyyar ciwowa daga ƙasashen waje. Yanzu kuma mun kasa samun inda za a ba mu wannan bashi.
An dai tsara cewa sabon titin jirgin zai keta jihohi 14 da su ka haɗa da Ribas, Abiya, Enugu, Benuwai, Nasarawa, Filato, Bauchi, Barno, da wayi yanki na Mahaɗar Kafanchan da Kaduna.
Sauran jihohin su ne Ebonyi, Anambra, Imo da Yobe.
Bashin da ake bin Najeriya ya yi katutu, wanda ko ta daina ciwo wani bashin, sai ta kai shekarar 2028 ba ta gama biyan bashin da Chana kaɗai ke bin ta ba, wanda aka karɓa iyar 2018 abin da ya yi shekarun baya.
Discussion about this post