A cikin saƙon murnar zagayowar ranar Kirsimeti a 2022, Babban Limamin Ɗariƙar Katoliƙa, Bishof Mathew Hassan-Kukah, ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana abin da ya kira alƙawurran ƙarairayin da Buhari ya yi. Sannan ya ce Buhari ya ƙara shiriritar da Najeriya da jefa ta cikin musiba, fiye da yadda ya same ta.
Kukah ya ce Buharin da aka yi tsammani idan ya hau a 2015 zai daƙile maciya rashawa da ɓarayin gwamnati, sai ya ɓuge da lulluɓe kan sa da babban bargon ɓarayin gwamnati.
Sai dai kuma ya jinjina wa Buhari dangane da wasu muhimman ayyukan da ya yi, musamman gina titina a faɗin ƙasar nan.
‘Buhari Ya Yi Nasarar Raba Kawuwan ‘Yan Najeriya’ – Kukah:
Kukah ya ce gwamnatin Buhari ta yi mummunan ƙaurin suna wajen fifita ƙabilar sa da nuna wariya ga sauran ƙabilu.”
Bishof Kukah ya ce babbar nasarar da Buhari ya samar ita ce raba kan al’ummar ƙasar nan. Ya ce ya sha faɗar haka a baya ya na maimaitawa.
“A fili kuma ƙuru-ƙuru kusan a kowane ɓangare ‘yar manuniya ta nuna yadda Buhari ya maida ƙasar mu ta koma ƙasa mai dauloli biyu: Daular Attajirai da Daular Faƙirai Matalauta maza da mata daga cikin kowace jam’iyyya, addinai, ƙabilu da sauran su.”
‘Cikin Ido Ake Tsawurya: Rashin Tsaro Ba Zai Hana Murnar Kirsimeti Ba’ – Kukah:
Kukah ya jinjina wa Kiristoci cewa Kirsimeti murnar ce ta shekara-shekara, wadda ke zowa ta wuce sai kuma wata shekarar. Saboda haka ya na jinjina masu ganin yadda gagarimar matsalar tsaro a ƙasar nan, ba ta hana a yi murnar Kirsimeti yi.
‘Mu Yi Wa Ɗimbin Waɗanda Ke Hannun ‘Yan Ta’adda Addu’ar Kuɓuta’ – Kukah:
A Najeriya a yau, ɗimbin mutane na can a hannun masu garkuwa da ‘yan ta’adda. Iyalan su kuma na cikin halin damuwa, ƙunci da tsananin tunani, a ƙarƙashin gwamnatin da ba ta ɗauki halin da su ke ciki da muhimmanci ba.
“To duk da haka, kada mu sare, kada kuma mu nuna tsoro, mu ci gaba da addu’a, mu jira hukuncin Ubangiji.
“Ga dama ta samu da za mu tsaya mu darje wajen zaɓen shugabanni nagari. Waɗanda idan mun yi kuka za su tsaya su saurare mu, su share mana hawayen mu.”
‘Gaskiya Ta Yi Ƙaranci A Najeriya, Sai Waskiya. An Saki Ubangiji An Kama Ubangida’ – Kukah:
A yanzu mun tsinci kan mu a cikin al’ummar da kusan kowane gwadaben da za ka bi ka kai inda gaskiya ta ke, ya lalace. ‘Yan gangan sun yi kaka-gida kan kowane gwadabe. Mu na cikin duniyar da mutum ke jefar da gaskiya, ya kama ƙarya. Ya bar tafarkin Ubangiji ya kama ubangida.”
‘Rashin Kyakkyawan Shugabanci Ya Bar Matasa Na Neman Nutsewa A Ruwa, ‘Yan Gangan Kuma Sun Ƙanƙame Rigunan Ceto Masu Nutsewa’ – Kukah:
“Mafi yawan ‘ya’yan mu sun afka cikin tarangahumar neman nutsewa a ruwa, su na ƙoƙarin ceto kan su tunda sun rasa mai ceton su. An bar su su na ta gaganiyar yadda za su tsira da rayukan su. Su kuma ‘yan gangan sai murna su ke yi da nishaɗi, tunda su na sanye da rigar ruwan da ko kwale-kwale ya kife, su ba nutsewa za su yi ba.”
‘Masu Cewa Ina Faɗa Da Arewa Ko Musulunci, Sun Kasa Ƙaryata Gaskiyar Da Ke Bayyanawa’ – Kukah:
“Ana yi min mummunar fahimta a wasu lokutan da na ke faɗar gaskiya, ana cewa ina faɗa da Arewa ko Musulunci. Amma kuma su masu yi min wannan yarfen, sun kasa ƙaryata gaskiyar da ke bayyanawa. Sun sun kasa fito da na su hujjojin da za su kayar da nawa hujjojin a ƙasa.
“Yanzu misali, Najeriya ta na da martaba da ƙima a duniya da Afrika kamar yadda ta ke da su a shekarun can baya? Shin a yanzu ƙarya na ke yi idan na ce Najeriya na sahun gaban ƙasashen da ake yawan kashe ɗan Adam a duniya? Shi ma wannan yawan kashe-kashen wani ci gaba ne? Ko kuwa idan na ce tulin bashi ya yi wa wannan gwamnati da Najeriya katutu shi ma ƙarya na yi?”
‘Buhari Ka Yi Ƙoƙari Wajen Gina Titina Da Jajircewar Inganta Matakan Zaɓuɓɓuka’ – Kukah:
“Yayin da na ke taya Shugaban Ƙasa da iyalan sa murnar zagayowar Kirsimeti, ina yi masa jinjina wajen da ya yi ƙoƙari, musamman ci gaban da ya samar a fannonin gina titina a faɗin ƙasar nan, da kuma ƙoƙarin da ya ke kan yi na ganin ya tsaftace matakan zaɓuɓɓuka a ƙasar nan. Ina yi maka fatan ƙara samun ƙoshin lafiya fiye da yadda ka ke a yanzu.
“Idan aka yi la’akari da dubban kilomitocin da ka shafe ka na tafiye-tafiye a duniya, za a ga cewa lallai ka na cikin ƙoshin lafiya.
” Sai dai kuma abin takaicin shi ne irin wannan damar da kai ka samu ta kula da lafiyar ka, ka kasa bai wa ‘yan Najeriya ita, kamar yadda ka yi masu alƙawari.
“Ba su da irin damar tafiye-tafiyen da ka ke yi, kuma za ka sauka ka bar su ba tare da ka daƙile cin hanci da rashawar da ka yi masu alƙawarin daƙilewa ba. Sai ma ƙara muni da wannan illa ta cin rashawa ta yi a ƙasar nan.
‘Yadda Ake Ƙoƙarin Wanzar Da Tafarkin Kyakkyawar Dangantaka Tsakanin Kiristoci Da Musulmai A Duniya’ – Kukah:
‘Yadda Fafaroma Ya Kai Ziyara Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Iraqi, Morocco Da Falasɗinu:
“Fafaroma ya kai ziyarar neman zaman lafiya cikin kyakkyawar zamantakewa tsakanin juna, samar da tsaro a tsakanin waɗannan mabiya addinan da su ka fito daga tsatson Ibrahimiyya. Kuma waɗannan ziyarce-ziyarcen da ya kai sun yi tasiri sosai.
‘Ƙoƙarin Shugaban Masar Wajen Inganta Kyakkyawar Zamantakewa Tsakanin Musulmai Da Kirista’ – Kukah:
“A yau Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya sanar da gagarimin ci gaban ƙulla kyakkyawar zamantakewa tsakanin Kiristoci Da Musulmai. Cikin 2019 ya gina katafaren Coci a Cairo, babban birnin ƙasar. Ya halarci tarukan addu’o’i a coci tare da Babban Limamin Kiristocin Cairo, Tawadros.
“A Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuwa an buɗe katafaren Cocin Cathedral na Our Lady of Arabia.”
A ƙarshe dai Kukah ya ja hankalin ‘yan Najeriya a yi koyi da irin wannan ƙoƙari da ake yi a duniya don samar da zaman lafiya tare da ɗorewar zamantakewa a tsakanin mabiya addinan biyu.
Discussion about this post