A ci gaba da samun goyon baya da ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na APC sanata Uba Sani ke yi a faɗin jihar, kungiyoyin mata daban-daban da ke jihar Kaduna sun bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar da yi masa alkawarin yi masa ambaliyar kuri’un su kaf a zaɓe mai zuwa.
A wani taro wanda dubban mata suka halarta tare da halarci sanata Uba Sani, shugabar jagorar matan Hajiya Rakiya, ta ce, jihar Kaduna ta yi dacen jarumi kuma haziki sannan gwarzo mai kishin jihar da kuma kishin talakawan jihar, wanda shine Uba Sani da ya fito takarar gwamna a jihar.
A na shi jawabin uban taro, kuma ɗan takara wato Uba Sani, ya mika godiyar sa ga wannan soyayya da yake samu daga wurin mutanen kauyen har Kaduna.
Wannan kungiya ta mata mai suna Jannah Foundation, karkashin jagorancin Hajiya Rakiya ta samu kyautar gudunmawar naira miliyan 20 daga Sanata Uba domin cigaba da gudanar da ayyukan na tallafi da take yi wa marasa karfi da talakawa.
Discussion about this post