Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa martaba da ƙimar Najeriya na ci gaba da zubewa warwas a nahiyar Afirka.
Obasanjo ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke jawabi wurin ƙaddamar da littafi mai suna THE LETTERMAN, wanda Babban Editan PREMIUM TIMES, Musikilu Mojeed ya wallafa.
Littafin, wato KUNDIN WASIƘUN SIRRIKAN OBASANJO, ya na ɗauke ne da wasiƙun da Obasanjo ya rubuta, tun daga lokacin da ya samu babban muƙamin soja, har bayan saukar da daga shugabancin ƙasa na mulkin dimokraɗiyya, cikin 2007.
Littafin dai ya ƙunshi shafuka 492, kuma an yi matuƙar mamakin ganin Obasanjo ya halarci taron ƙaddamar da littafin, domin da farko bai yi niyyar halarta ba.
Obasanjo ya ce Najeriya ta rasa girma da martabar ta, ta yi sakanci wasu ƙasashe ciki har da Qatar ta riƙe ragamar, inda ya bada misali da rawar da Qatar ta taka a Chadi bayan mutuwar Idris Deby, Shugaban Ƙasar.
‘Mojeed Bai Ce Min Littafi Zai Rubuta Da Tulin Wasiƙu Na Ba’ – Obasanjo:
Obasanjo ya jinjina wa marubucin littafin, wanda ya ce bai taɓa bayyana masa cewa littafi zai rubuta da tulin wasiƙun ba.
Haka kuma Obasanjo ya riƙa bayyana muhimmancin wasu wasiƙun da ya rubuta tun tuni, waɗanda sai a cikin littafin ya sake karanta su.
Da ya koma kan zubewar darajar Najeriya a Afrika, Obasanjo ya ce “a shekarun 1970s da 1980s, duk wani abin da Amurka za ta yi a Afirka, sai ta shawarci Najeriya tukunna.”
“Amma ta ya aka yi mu ka lalace haka? Na ji an ce baya-bayan nan da aka harbe Idris Deby na Chadi, Qatar ce ta shiga ta fita a sasanta al’amurra. Amma ga Najeriya na iyaka da Chadi, ba ta yi komai ba,” inji Obasanjo.
‘Mojeed Ya Shammace Ni, Ban Yi Niyyar Halartar Ƙaddamar Da Littafin Ba’ – Obasanjo:
Obasanjo ya ce ya kashe wani muhimmin uziri da ya ke da shi a Habasha, ya zo wurin gabatar da littafin, saboda muhimmancin sa.
“Saboda marubucin littafin bai nemi umarni na ko amincewa ta kafin a buga littafin ba.
“Ban san komai ba sai kawai ya kawo min kwafe biyu na littafin. Sai da na gama karantawa, na ce lallai ba za a bar ni a baya wajen taron gabatar da littafin ba.”
Discussion about this post