Shugaban APC na Jihar Ribas, Emeka Beke, ya koka a kan yadda wasu manyan APC ke amsa gayyatar Gwamna Nyesom Wike, su na jihar su na zubar da ƙimar jam’iyyyar su a jihar.
Beke ya na magana ne kan wasu jiga-jigan APC da Nyesom Wike ke gayyatowa idan zai buɗe wani gagarimin aikin da gwamnatin sa ta PDP ta gina.
Shugaban na APC a Ribas, ya ce waɗanda ake gayyatowar su na zuwa su na yabon gwamnatin Wike ta PDP, a gefe ɗaya kuma su na kushe APC, jam’iyyar su.
Cikin wasiƙar ƙorafin da Beke ya aika wa Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu, Beke ya buga misali da abin da ya kira kwafsawar da tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole da kuma Gwamna David Umahi na Ebonyi.
Beke ya nemi su biyu su fito su bayar da haƙuri, ko kuma a dakatar da su daga APC zuwa wani lokaci.
“Kwanan nan Wike ya gayyaci Adams Oshiomhole wurin buɗe gadar sama. A wurin taron saboda kwaɗayin abin da Wike zai ba shi, Oshiomhole ya ci mutuncin APC.
“To mu ba mu hana mutum ya zo maular sa ba. Amma idan ka karɓa, ba sai ka kushe APC a gaban Wike ba.
“Oshiomhole cewa ya yi ‘na da dalilin da ya sa APC ba ta iya lashe kowane zaɓe a Ribas. Ashe wasu zarata kuma ƙwararrun matasa ne Wike ya ɗora su na aiki gajirga, kuma duk inda zai je da su. Har Edo ma da su ya je.”
“Gwamna David Umahi na Ebonyi ma da ya zo buɗe titin Akepalu zuwa Egbeda a ranar 22 Ga Nuwamba, 2022, cewa ya yi, “Daga yau ba zan sake zuwa Ribas ba, sai fa a kamfen ɗin shugaban ƙasa. Saboda na san dukkan sauran zaɓukan Ribas, duk PDP ce za ta lashe su.” Inji Beke.
Discussion about this post