Bayan komawar Shugaba Muhammadu Buhari fadar sa, tun bai gama hutun gajiya daga zuwa Bauchi wurin ƙaddamar da fara aikin haƙar ɗanyen mai a yankin Kolmani da ke Bauchi da Gombe ba, wasu baƙin ‘yan bindiga da ke ɗauke da zabga-zabgan bindigogi na zamani, har da samfurin tashi-gari-barde su ka kai harin fatattaka, kisa da garkuwa a kusa da inda Buhari ya buɗe cibiyar rijiyar fara aikin haƙar ɗanyen mai a cikin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri.
Kisa, fatattaka da garkuwar da ake yi bakatatan a yankin da Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano akwai ɗanyen mai a wurin, ya tilasta dubban mazauna ƙauyukan kewayen tserewa daga cikin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri, Jihar Bauchi.
Wanda ya tsere da kyar na gudun kada a kashe shi, ko a yi garkuwa da shi.
Wasu baƙin ‘yan bindiga ne da ba a san daga inda su ke ba, su ka addabi mazauna garuruwa sama da 20 su na kai masu hare-hare a cikin ƙaramar hukumar.
Farmakin garkuwa har ya dangana da kusa da inda Buhari ya ƙaddamar da cibiyar fara aikin haƙar ɗanyen mai.
Jami’ai a ƙaramar hukumar sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa aƙalla an kashe mutum 10, kuma a kullum ana damƙe mazauna yankin ana garkuwa da su. Dubban mutane kuma su na ta tserewa daga ƙauyukan su, zuwa cikin garin Alƙaleri har da wasu garuruwa cikin jihar Gombe, saboda tsira da rayukan su.
Sa’idu Jibrin, wanda shi ne Kansilan Mazaɓar Maimaɗi, ɗaya daga cikin mazaɓun da ‘yan bindigar ke kai wa matsin-lambar hare-hare, ya shaida wa wakilin mu cewa ‘yan bindigar na kai masu hare-hare da farmaki kai-tsaye, babu wani hoɓɓasan daƙile su da jami’an tsaro ke yi
“Yanzu a yankin mu garkuwa da mutane ana karɓar kuɗaɗe ya zama ruwan-dare. Cikin ƙasa da kwanaki 20, an yi garkuwa da mutum kimanin 30, an biya kuɗin fansa za su kai Naira miliyan 2. Kuma sun kashe aƙalla mutum zai kai 10.
“Yanzu yankin ya samu albarkatun ɗanyen mai, don haka mutane daga sassa daban-daban za su wo mana caa. Sai dai kuma babu wanda zai so zuwa ya zuba jarin sa sai fa idan akwai ƙwaƙƙwaran tsaro a yankin.
“Yan bindiga sun je har wurin da aka ƙaddamar da cibiyar fara aikin haƙar ɗanyen mai, su ka kama wani maigida, wanda gidan sa bai kai tazarar kilomita ɗaya daga wurin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙar ɗanyen mai ba.
“An kai wannan harin bayan Shugaban Ƙasa ya kai ziyarar fara aikin ya koma fadar sa. An kuma kwashi wasu mutum biyu a daidai wurin an arce da su.
“An kashe mutum a Mai-Arin Kudu, an yi garkuwa da matar sa. A Zadawa kuma sun kashe shugaban matasan ƙauyen. Mun dawo daga Gombe kenan, su ka bindige shi. Bayan ya mutu kuma su ka ƙara yi masa harbi bakwai, su ka tafi da mahaifiyar sa da ƙanuwar sa.
“A Mai-Arin Aware kuwa, sun kashe mahaifin wani yaro, kuma su ka tafi da yaron. A ƙauyen Garfatu kuma sun bindige shugaban ‘yan bijilante, su ka arce da ‘yar sa,” inji kansilan.
“Mazauna yankin sai tserewa su ke yi su na kwarara wasu garuruwa. Mazaunan na ganin lamarin na da nasaba da ɗanyen man da aka ce an gano a yankin, amma abin ba haka ba ne,” inji Jibrin.
Ya ce Ƙaramar Hukumar Alƙakeri ta yi iyaka da Yankari Dajin Gwamnati, wanda kusan babu dajin gwamnati a ƙasar nan da ya kai na Yankari faɗi da girma. Ya ce maharan a cikin dajin Yankari su ke a ɓoye.
“Waɗannan ‘yan bindiga fa baƙi ne, amma su na amfani da mutanen da ke cikin jama’a, su na gulmata masu abin da ke faruwa idan za su kai hare-haren su.
Fiye Da Mazauna Gidaje Dubu Ɗaya Ne ‘Yan Bindiga Su Ka Kora A Yankin Da Ɗanyen Mai A Bauchi:
Wannan yanki ya na da gundumar hakimai uku, wato Pali, Gwana da Duguri. Kiwane basaraken kuwa ya na ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ne.
To filin da aka ce ɗanyen man fetur ya ke, ya na ƙarƙashin yankin Pali ne. Amma mazauna yankin na ta yin tururuwar barin wurin su na gudu zuwa cikin garin Alƙaleri, wasu na tserewa zuwa Musau, wasu kuma har cikin Jihar Gombe.
Wani mai riƙe da sarautar gargajiya wanda ya ce wa wakilin mu kada a ambaci sunan sa, ya ce aƙalla mutane daga cikin gidaje dubu ɗaya sun arce, saboda tsoron ta’addancin ‘yan bindiga.
Ya ce ƙauyukan da abin ya shafa a gundumar Pali, sun haɗa da Jada, Mai Arin Kudu, Dani, Kufa, Bubu, Papa, Kuturun Kuka, Tudun Wadan Jada, Zadawa da Bambu.
Ya ce lamarin ya ritsa da garuruwa irin su Gachiri, Maimaɗi, Shugu, Garfatu, Mai Arin Arewa, Dakai, Maso Kano, Kwanan Kuka, Yola da Bakin Ruwa.
A gundumar Gwana kuwa, lamarin ya shafi garuruwan Mansur, Baladde, Masaga, Gurabayi, Diji, Bunga, Gwanan Dutse, Sabon Garin Bagobiri, Garin Bano, Jamari, Garin Juba.
Ya ce akwai kuma Kwalkwal, Sankali, Alƙali Sule, Kargo, Digare, Gobirawa da Yalo.
Hare-hare A Yankin Ɗanyen Man Bauchi: ‘Yadda Jami’an Tsaron Ke Karɓe Wa Masu Hijira Kuɗaɗen Su – Wani Basarake:
Wannan basaraken ya bayyana wa wakilin mu takaici da damuwar sa, dangane da jami’an tsaro ke kuɗancewa ta hanyar karɓar kuɗaɗe daga masu gudun hijirar da ke tserewa daga yankin da aka ce an gano ɗanyen mai. Waɗannan jami’an tsaro, su ne masu tsaron shingayen kan titi a wurare daban-daban.
Ya ce masu tserewa zuwa Gombe sai sun bi ta aƙalla shingayen jami’an tsaro har wurare 10.
Ya ce a garin Futuk kaɗai akwai shingaye uku. Kuma aƙalla duk fasinjojin da ke cikin mota ɗaya, su na haɗa wa jami’an da ke kowane shinge Naira 10,000.
Yunƙurin Mamaye ‘Yankin Da Aka Gano Ɗanyen Mai: Lamarin Ya Fa Yi Muni Matuƙa – Ɗan Majalisar Tarayya na Alƙaleri/Kirfi
Honorabul Musa Mohammed ya ce tabbas lamarin ya yi muni sosai. Amma ana ta ƙoƙarin ganin an magance matsalar.
Ya ce a matsayin sa na Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, ya kai rahoton ga gwamnati domin a ɗauki mataki.
Ya ce idan jami’an tsaro su ka haɗu daga ɓangaren Bauchi da Filato, za a iya shawo kan lamarin.
Discussion about this post