Majalisar wakilai ta tarayya ta bukaci gwamnati ta saka darasin koyar da cin hanci da rashawa a cikin darusan da ake koyarwa a makarantun firamare da sakandare a kasar nan.
Kakakin majalisan Femi Gbajabiamila (APC, Lagos), Aisha Dukku (APC, Gombe) da wasu ‘yan majalisa biyu jagorancin tattaunawar a zauren majalisa a cikin makon jiya.
A madadin sauran ‘yan majalisan da suka goyi bayan wannan kudiri Aisha ta bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan matsala ce da ta ki ci ta ki cinyewa.
Ta ce a dalilin haka ya kamata a dauki tsauraran matakai domin kawar da matsalar.
“ Najeriya ba ta iya kawar da matsalar cin hanci da rashawa ba saboda rashin daukar tsauraran matakan da suka kamata domin kawar da wannan matsala, mai makaon haka sai da da samun wurin zama ta ke yi a kasar.
“Koyar da dalibai wannan darasi a makarantun kasar nan zai taimaka wajen wayar da kan su tun suna yara wajen nisantar cin hanci da rashawa kafin su girma su zama manyan gobe.
Aisha ta ce wannan kudirin zai yi aiki ne idan an samu goyan bayan duk masu ruwa da tsaki a kasar.
A zauren ‘yan majalisa da dama sun goyi bayan wannan kudiri sannan majalisar ta mika shi ga kwamitin ilimi nauyin ganin wannan kudirin ya fara aiki a kasar nan ta yanhar aiki akai cikin gagggawa.