Mai martaba sarkin Birnin Gwari, Zubairu Maigwari II ya naɗa Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, sarautar ‘ Dakaren’ Birnin Gwari.
Maimartaba Maigwari II ya naɗa Tinubu a fadar sa dake Birnin Gwari ranar Litinin inda ya gode masa bisa ziyarar da ya kawo wa masarautar.
A cikin tawagar Tinubu akwai gwamnan Jihar Kaduna wanda shine jagorar tafiyar sannan kuma da gwamnonin Filato, Kano da sauran gaggan ƴan siyasa na jam’iyyar APC.
Bayan haka ƴaƴan jam’iyyar tare da duka ƴan takaran sun dunguma filin wasa na Ahmadu Bello, ranar Talata inda Jam’iyyar ta kaddamar da kamfen din ta na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a Kaduna.
A wannan gangami ne aka kaddamar da ɗan takarar gwamnan jihar na APC, Sanata Uba Sani ga mutanen jihar.
Filin wasa na Ahmadu Bello ya cika ya batse famda masoya da kuma magoya bayan jam’iyyar APC.
Discussion about this post