Sashen kula da tsaftace muhalli na Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ya rusa gine-gine 3,197 da aka gina ba bisa tsari ba sannan ya markade babura 1,292 a cikin kwanaki 14 da suka wuce.
Shugaban wannan sashe Shehu Ahmad ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Ahmad ya ce hukumar ta yi haka ne domin kara tsaftace muhalli sannan da samar da tsaro wa mutane a Abuja.
“ Mun rusa gine-gine 123 da aka gina ba bisa ka’ida ba a Katampe Extension da Guzape sannan muka rusa bukkoki 3,074 a Durumi I, II, III, Monkey Village, Dagba, sansanin ‘yan gudun hijira dake Durimi da wasu matsugunan da aka gina su a karkashin gadoji a Abuja.
“ Daga nan kuma mun lalata babura 1,292 da muka kama a sassan Abuja da doka ta hana ‘yan achaba aiki.
Ya ce hukumar ta yi duk wadannan aiyuka ne daga ranar 9 zuwa 22 ga Disambar 2022.
Ya ce Guzape, Katampe Extension, Durumi, Wasa, Kuchi Goro da Lugbe hanyar tashar jiragen sama na daga cikin wuraren da suka rusa gine-gine da aka kafa ba bisa doka ba.
Sannan hanyar tashar jiragen sama, Durumi, Kubwa, Asokoro Extension da Guzape na daga cikin wuraren da suka kama babura.
Discussion about this post