Ministan Yaɗa Labarai da Inganta Al’adu, Lai Mohammed, ya ragargaji tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, dangane da furucin da Atiku ɗin ya yi kan gwamnatin APC a taron kamfen ɗin sa na Akure.
A ranar Laraba ce dai Atiku ya hau duro a jihar Ondo, a kamfen ɗin sa na takarar shugaban ƙasa a PDP, ya yi iƙirarin cewa wannan gwamnatin ta APC ba ta tsinana wa ‘yan Najeriya komai ba.
Atiku: “Ai mutum ba ma zai iya kwatanta abin da PDP ta yi tsawon shekaru 16 ba da abin da APC ta yi cikin shekaru 8. Saboda APC ba ta yi komai ba,” inji Atiku.
Da ya ke mayar wa Atiku da martani, Lai Mohammed ya ce, “babu yadda za a yi Atiku ya san irin ayyukan da APC ta yi, domin shi kacokan ya koma Dubai da zama. Bai san komai a Najeriya ba.
Minista Lai ya ce kawai dai Atiku na ƙoƙarin dankwafar da ayyukan da wannan gwamnati ta yi, “saboda yunwa da kururun neman mulki da ya ke yi ido-rufe.”
“A shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki, shekaru 8 da Atiku aka yi su, lokacin ya na mataimakin shugaban ƙasa. Amma har ya sauka babu kwalta wadda motoci za su riƙa shiga ƙauyen su. Ta lalace PDP ba ta gyara ba. Sai a mulkin APC aka gyara masu titin, har Atiku na hawa ya na zuwa garin su.”
Lai ya ce akwai ƙananan hukumomi a shiyyar Atiku can jihar Adamawa, waɗanda ke da yalwar kayan abincin gona, waɗanda kafin APC ta hau mulki a 2015, yankunan ba su shiguwa cikin daɗi da mota. Sai da APC ta hau ne ta samar masu da sabbin titina.
“APC ta gina titin Mayo Belwa zuwa Jada zuwa Ganye zuwa Toungo. Yanzu Atiku har Jada ya ke iya zuwa can mahaifar sa, saboda APC ta yi masu titi.” Inji Lai.
Da ya koma kan matsalar tsaro, Lai ya ce a lokacin PDP akwai ƙananan hukumomi biyar na Jihar Adamawa da ke hannun Boko Haram, waɗanda an ragargaza ofisoshin ‘yan sanda, asibitoci, makarantu da kasuwanni. Wato ƙananan hukumomin Michika, Madagali, Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, Gombi, Maiha da Hong.
“Amma a yanzu ko fuloti ɗaya babu a hannun ‘yan Boko Haram.”
“A wancan lokacin ko gida Atiku ba ya iya zuwa. Lokacin da wani makusancin sa Mista Adila ya rasu a kisan da ‘yan Boko Haram su ka yi masa, Atiku kasa zuwa ya yi.” Inji Lai.
A ƙarshe Minista Lai Mohammed ya ce, “idan mai fitsarin kwance ya na da kunya, ba zai riƙa aibata wanda ya wanke karifar da ya jiƙe da fitsarin ba.”
Daga nan ya tunatar da Atiku cewa matasan Adamawa 29,641 suka ci moriyar N-POWER. Yara 162,782 a Adamawa su ka ci moriyar tsarin ciyar da ɗaliban firamare, wanda har masu dafa abinci su 2,259 aka ɗauka a faɗin jihar.
Yayin da ya ce ‘yan Adamawa 64,607 su ka ci moriyar Trader Moni, wasu 38,000 su ka amfana da tallafin Market Moni.
Discussion about this post