Kwamitin Binciken Yadda Shugabannin Cibiyoyi, Hukumomi da Ma’aikatu ke kashe kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya nemi a kamo masa wasu manyan jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari su 54, bayan sun ƙi yi wa Akanta Janar na Tarayya bayanin yadda su ka kashe wasu kuɗaɗe daga 2014 zuwa 2018 da kuma daga 2019 zuwa 2021.
Waɗanda ake so a kama ɗin waɗanda cikin su har da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, bayan sun ƙi yi wa Akanta Janar bayanin yadda su ka kashe kuɗaɗen, kuma sun ƙi amsa gayyatar da shi Kwamitin na Majalisar Tarayya ɗin ya yi masu dangane da binciken su da ake yi.
Shugaban Kwamitin Binciken Honorabul Oluwole Oke, ɗan PDP daga Jihar Osun, shi ne ya rubuta bayanin neman a kamo manyan jami’an su 54, a cikin rahoton da ya gabatar wa majalisa, a ranar Alhamis.
Ga Rahoton Nan:
“Rahoto Kan Kasa Bayyanar Wasu Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati Zuwa Su Bayar da Rahoton Yadda Su Ka Kashe Kuɗaɗe Daga 2014-2024 da 2019-2021 Wurin Akanta Janar na Tarayya.”
Baya ga Emefiele na CBN, hukumomi irin su NNPC, NDDC da RMAFC.
Shi dama wannan kwamiti a majalisa, akasari ɗan jam’iyyar adawa ce ke shugabancin sa.
A cikin rahoton, an ce sammacin a kamo zai sa tilas su tilas a cikin mako ɗaya su bayyana a gaban kwamiti, kamar yada Sashe na 89 na Dokar Najeriya ta 1999 ya tanadar.”
Haka nan kuma rahoton ya nemi a hukunta ma’aikatu ko hukumomin da su ka aika wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya rahotannin su a makare.
Akwai HNSA, Jami’ar Jos, Jami’ar Ilorin, FMC Umuahia da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure.
Sauran sun haɗa da Jami’ar Gusau, Babbar Kwalejin Tarayya ta Kazaure, ta Asaba, ta Obudu da Jami’ar Koyon Dabarun Noma ta Makurɗi.
Akwai Asibitocin Gwamnatin Tarayya na Ado-Ekiti, Lokoja da wasu da dama.
Akwai NIMASA, Bankin Bayar Jingina na Mortgage Bank, Hukumar Gidajen Gwamnatin Tarayya (FHA), wadda kwamitin ya ce rabon da hukumar ta gabatar da yadda ta ke kashe kuɗaɗen ta a duk ƙarshen shekara, tun 2003.
Cikin hukumomin da kwamitin ya nemi a hukunta har da NDLEA.
Discussion about this post