Mai Shari’a a Babbar Kotun Asaba a Jihar Delta, ya tona asirin yadda Hukumar NDLEA ta ɓoye wasu kadarorin da ta ƙwace daga hannun masu fataucin ƙwayoyin da aka ɗaure a kurkuku.
Sai dai kuma NDLEA ta ƙaryata wannan zargi da kotun ta yi mata, a cikin wata hirar da hukumar ta yi da PREMIUM TIMES.
Wannan jarida ta ruwaito yadda Mai Shari’a Okon Abang ya ɗaure wasu fataken muggan ƙwayoyi ɗaurin shekaru 9 da kuma mai ɗaurin shekaru 10 a ranar Talata, sannan kuma ya ragargaji NDLEA saboda ta toshe ƙofar yadda kotu za ta iya yi wa fataken ƙwayar hukunci mai tsanani.
Fataken ƙwayar da kotu ta ɗaure sun haɗa da ‘yan Najeria su biyar, Anthony Umolu, Chibi Aruh, Izuchukwu Anieto, Williams Agusi da kuma Koisichukwu Umolu. Sauran kuma sun haɗa wasu riƙaƙƙun fataken ƙwaya daga Mexico, waɗanda a duniya ake neman su ruwa a jallo a faɗin duniyar nan.
‘Yan Mexico ɗin sun haɗa da Cervatos Bruno, Rivas Pastiano, Castillo Cristobal da Patida Pedro.
An damƙe a cikin watan Maris 2016, a wani ɗakin haɗa magunguna na cuwa-cuwa a Asaba, babban birnin jihar Delta, inda su ka haɗa wata ƙwayar da ke kama da hodar Ibilis. Hujjoji sun gano cewa mutanen su ka da wani gungu ne na fataucin muggan ƙwayoyi.
Mai Shari’a Abang ya yi tir da Hukumar NDLEA, saboda ta cimma yarjejeniyar sasantawa da fataken ƙwayoyin a lokacin da ake tsakiyar shari’ar mutanen da aka shafe shekaru shida ana fafatawa a kotu, kuma har kotun ta tabbatar da rashin gaskiyar su.
An daidaita da fataken ƙwayoyin da NDLEA za a ƙwace wasu kadarorin su ɗungurugum, waɗanda su ka haɗa da mota ƙirar Marsandi ML350, Toyota Tundra Hilux da kuma naira miliyan 20 sai naira N894,463.43 waɗanda aka samu a hannun su.
A ranar Talata dai Abang ya ce a gaggauta damƙa kayayyakin da kuɗaɗen ga gwamnatin tarayya. Ya ce a kai kuɗin a CBN a ajiye cikin Asusun Gwamnatin Tarayya kafin nan da ƙarshen kwanaki 30.
Mai Shari’a ya ce baya ga neman sassauci ga fataken da NDLEA ta yi, ya ce a cikin yarjejeniyar da su ka yi da NDLEA babu batun kadarori da kuɗaɗen da NDLEA ta karɓe a wurin fataken ƙwayoyin.
“NDLEA ta ƙulla yarjejeniyar ce da fataken a ranar 30 Ga Yuni, 2022.” Inji Abang.
Abang ya ce sannan kuma NDLEA ba ta gabatar da muggan ƙwayoyin da ta kama a hannun fataken ba, kuma ba ta gabatar wa kotun shaidu na kayan aikin da ta kama a ɗakin haɗa muggan ƙwayoyin ba.
Kadarorin da aka ƙwace waɗanda NDLEA ba ta bayyana wa kotu ba, sun haɗa da filaye a Legas, Ogun da Anambra, sai gida a Abuja.
Discussion about this post