Gwamnatin Najeriya ta janye dokokin Korona wanda aka saka wa matafiya bayan an samun raguwar yaduwar cutar a duniya.
Wasikar da hukumar NCAA ta aika wa masu ruwa da tsaki a fannin jiragen sama da jiragen Saman kasar nan ya tabbatar cewa Najeriya da sauran kasashen duniya sun samu raguwan yaduwar cutar.
A wasikan wanda ke da kwanan wata 12 ga Disamba da ref no. NCAA/DG/AIR/11/16/358 ya nuna cewa shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar ta kasa PSC Boss Mustapha ya amince a sassauta dokokin Korona.
Takunkumin fuska
Yanzu dokar dakile yaduwar cutar Korona ya ce ba dole bane ma’aikatan tashar jiragen sama da fasinjoji su rika sa takunkumin fuska ba a haraban tashar jiragen saman, wajen shiga jirgi ko Kuma a cikin jirgin amma idan har mutum na bukatan takunkumin fuskan zai iya sakawa domin samun kariya.
Dokan ya Kuma ce tsofaffin da suka dara shekaru 60 ko suna dauke da wasu cututtuka za su iya ci gaba da amfani da takunkumin fuska tare da nisanta kansu daga taron mutane su rika wanke hanayen su da ruwa da sabulu ko Kuma da man tsaftace hannu.
Dokan ya kara cewa yi jakunkunan matafiya feshi domin kashe kwayoyin cutar kafin a shiga jirgi bai zama dole ba.
Daga yanzu duk wuraren da ake siyar da abinci da abin sha a tashar jiragen sama za ci gaba da aiki.
“Nisanta Kai daga taron mutane a harabar jiragen sama bai zama dole ba amma tashar jiragen za ta ci gaba da tafiyar da aiyukkan ta tare da tsaftace muhalinta da kafa wuraren wanke hannu domin fashinjoji da ma’aikata.
Yin gwajin cutar
Ba dole bane matafiya su gabatar da takardar gwajin cutar Korona kafin su shiga jirgi ko bayan sun sauka daga jirgi.
Sannan ba dole bane wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar Korona ba ko ba su kammala yin allurar rigakafin ba su killace kansu na tsawon kwanaki 7 tare da gabatar da sakamakon gwajin cutar da ya nuna cewa basu dauke da cutar bayan sun dawo daga tafiya..
Cika fom kafin a yi tafiya
Daga yanzu bas dole bane matafiya su nemi takardan izinin yin tafiya ba domin yanzu za su iya yin tafiya su idan sun cike fom din lafiya a shafin NITP a yanar gizo.
Idan matafiyi bai cika fom din ba zai iya cikewa yayin da ake tafiya a jirgi ko Kuma da zaran ya zauka daga jirgin.
Yaduwar cutar Korona a Najeriya
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 266,283 be suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,155 a jihohi 36 da Abuja.
A ranar 9 ga Disemba alkaluman yaduwar cutar sun nuns cewa mutum 59,867,077 ne suka kammala yin allurar rigakafin Korona sannan mutum 12,403,486 ba su kammala yin allurar rigakafin ba a Najeriya.
Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa NPHCDA ta ce zuwa yanzu mutum kashi 35% be suka rage da ba su Yi allurar rigakafin cutar ba.
Sannan ya rage wa gwamnati ta Yi wa mutum miliyan 18.5 allurar rigakafi kafin ta iya cin ma burin ta na Yi wa mutum kashi 70% allurar rigakafin cutar daga nan zuwa ranar 31 ga Disemba 2022.
Discussion about this post