Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya lashi takobin fatattakar fatara da talauci a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Tinubu, ya bayyana haka ne a taron da yayi da masu faɗa aji da mutanen garin Calabar, Jihar Cross Rivers.
Tinubu ya ce ” Ina tabbatar muku da cewa idan na zama shugaban kasa a Najeriya, zan fatattaki talauci da fatara. Ƴan Najeriya za su yi sallama da talauci.
” Ni da kuke gani gogarman dambe ne amma ba dambe da mutane nake yi ba, abinda na saka a gaba shine kawai a samu ci gaba a Najeriya kowa ya wataya, ayi bankwana da talauci.
Burina na ci gaba da ciyar da Najeriya gaba shi ne kawai dalilin da ya sa nake yin takara; babu wani mutum da ya ke tsole min ido ko nake fargaba.
“ Duk sauran ƴan takaran ba su da gaskiya; ba za su iya cika alkawuran da za su ɗauka ba; abin da suke so shine kawai su ci zaɓe su yi abinda da suka ga dama.
” Allah ya yi wa Najeriya albarka da mutane da da kuma arziki a duk jihohin kasar nan. Kowace jiha na da arzikin da idan muka yi nasara za mu bi jiha jiha muna bunkasa arzikin da ke wannan jiha domin amfanin mutanen jihar da kasa bake ɗaya.
A jawabin sa mai masaukin baki, kuma gwamnan. Jihar Cross Rivers, John Ayade ya jinjina wa Tinubu da kuma yin kira ga mutanen jihar da su fito kwansu da kwarkwara su mara masa baya a lokacin zabe.
Discussion about this post