Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi hukumar zaɓe cewa kada su kuskura su kawo wa ƴan Najeriya wani dalili da zai sa a ce wai an samu matsala wajen gudanar da zaɓe a 2023.
Shugaba Buhari wanda ya bayyana a tattaunawa da yayi da wasu masu ruwa da tsaki a kasar Amurka, ya ce ƙarkashin sa za a tabbata an gudanar da zaɓe mai nagarta kuma sahihi wanda kowa zai yi alfahari da shi .
” Ina so in tabbatar muku cewa hukumar zaɓe a shirya take, domin na tabbatar da an basi duk kuɗaɗen da suke bukata don ganin an gudanar da zaɓen yadda ya kamata ba tare da an samu wata matsala ko tangarɗa ba.
Shugaba Buhari ya ce idan aka lura za a ga cewa tun daga 2015, zaɓuka a Najeriya ya rika kyau saboda kokarin da ya yi na ganin kuri’un ƴan ya yi tasiri.
Daga nan sai ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su taimakwa wa Najeriya da ma yankin Afirka domin ganin an inganta harkokin zaɓe da kuma bunƙasar tattalin arzikin yankin.
Najeriya dai na cigaba da shirin gudanar da babban zabenta wanda za a yi a watannin Faburairu da Maris ɗin 2023.
Jam’iyyu musamman manyan na kasar na cigabad a gudanar da kamfen da yi wa mutane alkawurra domin samun amincewar su a lokacin kaɗa kuri’a.
Wannan karon babu shugaba Buhari a cikin jerin ƴan takara, akwai yiwuwar a samu sauye sauye na sasarorin da ƴan takara sasu samu zaɓen ba kamar yadda APC ta rika samun ambaliyar kuri’u ba a dalilin Buhari da yake shima yana takara ba