Hukumar NDLEA ta bayyana cewa ta kama muggan kwayoyin da aka shigo da su kasarnan da suka hada da Tramadol, ganyen wiwi, Diazepam da Exol a jihar Katsina.
Shugaban hukumar reshen jihar Katsina Mohammed Bashir ya sanar da sanar da haka ranar Talata a garin Katsina yayin da yake gabatar da wasu mutane uku dake da hannu a safarar muggan kwayoyi da hukumar ta kama.
Ya ce hukumar ta kama muggan kwayoyin da wadannan mutane a lokacin da jami’an hukumar suka kai samamme wuraren da aka safara da kasuwancin su a Katsina.
“Yanzu hukumar ta kara mai da hankali wajen karfafa bincike da bin wuaren da ake harkallar kwayoyi a jihar musamman yanzu da ake shirin bukin Kirisimati da zaben 2023.
“ Abin da zai ba ka tsoro shine yadda sai a irin wannan lokaci na Kirismeti kwayoyi irin haka ke yawaita a hannun mutane. hakan ya sa dole yanzu jami’an mu za su kara kaimi wajen zazzagayawa da kamo masu harkallar wannan abu.
“ A ranar 12 ga Disemba ma’aikatan mu sun kama wata mota dauke da ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 4.5 da kwayan Tramadol mai nauyin kilogiram kilo 2.5.
“Ba karamin barna za a samu ba idan da wadannan kwayoyi sun wuce sun shiga hannun mutane musamman a wannan lokacin na bukukuwan Krisimati da shirin zaben 2023 da ake yi.
“A ranar 5 ga Disemba ma’aikatan mu sun kama wani direba dauke da kwayoyin Diazepam mai nauyin kilogiram 4 da Exol mai nauyin kilogiram 20 a hanyar Malumfashi zuwa Zaria.
“Zuwa yanzu hukumar na gab da kammala bincike akan wadannan mutane sannan idan ta kammala za ta maka su a babban kotu a Katsina.