Sakataren Kwamitin shugaban kasa kan binciken harkallar naira Tiriliyan 87 na Stamp Duty wanda ake zargin gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya tafka tare da wasu, Gudaji Kazaure ya bayyana wa manema labarai cewa shugaban Muhammadu Buhari ya bashi damar ya tsige gwamnan babban bankin Najeriya.
Da yake jawabi tare da manema labarai a ofishin sa a majalisar tarayya, Kazaure ya ce wasu ne suka rika yi wa kwamitin bita-da-kulli don ganin ba a bincike wadanda suka yi sama da fadi da wadannan kudade ba.
” Ni da kaina na gana da shugaban Buhari, mutumin kirki, kuma ya bani damar lallai a gudanar da wannan bincike, domin kudaden da yawan gaske. naira triliyan 87 aka yi ruf da ciki da su na Stamp Duty. sannan kuma kullum ana cewa kasa babu kudi.
” Buhari da kan sa ya ce idan za a iya bankado harkallar wadannan kudade, za aiya biyan duka basukan da ake bin Najeriya, sannan a yi ayyuka har ma a jiye wa gwamnati mai zuwa wani abu.
Bayan haka mun gayyaci gwamman babban bankin, ya zo ofishin kwamitin mu da ke hedikwatar SSS, ko da ya bayyana sai ya rika cewa wai bashi da lafiya, domin mun tsare shi har na awowi 4 a ofishin. Ba mu yarda ya tafi gida ba sai da aka amince aba shi beli ta musamman, saboda ya samu damar wadata mu da wasu takardu domin aikin mu.
Gudaji Kazaure ya ce ” Kudi ne masu yawan gaske da ba asan da su ba, aka waske da su. sannan aka ja baki aka yi shiru. Wadannan kudade za su iya biya wa Najeriya duk basukan dake binta sannan su gama ayyukan da ake yi na cigaba kuma a ajiye wa gwamnati mai zuwa kyakkyawar tanadi.
Kazaure ya ce CBN, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, sai kuma Manyan Hadiman Fadar Shugaban Ƙasa sun yi masa katanga, su ka hana shi ganin Shugaban Ƙasa, domin ya yi masa bayanin abin da binciken kwamitin sa ya gano.
Gudaji, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa, ya ce kwamitin sa ya zargi hukumomi da cibiyoyin gwamnati da laifin yi wa kwamitin sa zagon ƙasa.
Ya ƙara da cewa kwamitin sa ya bankaɗo cewa zunzurutun naira tiriliyan 89 ne aka karkatar, daga kuɗaɗen harajin da bankuna ke cirar wa gwamnati daga masu hulɗa da bankuna, wato stamp duties.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, ya ce wannan zargi na Gudaji Kazaure shafa-labari-shuni ne kawai, ba gaskiya ba ce.
Shehu ya ce ai dokar ƙasa ma ta haramta wani ɗan majalisar tarayya ya yi sakataren kwamitin da manyan jami’an gwamnati ke ciki.
Shehu ya ce ai tuni aka rushe kwamitin da shi Gudaji Kazaure ya ce shi ne sakataren kwamiti.
Sai dai kuma ya ce akwai kuma wani kwamiti wanda Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ke shugabanta, wanda aka kafa cikin Juni, 2020, wanda aikin kwamitin shi ne tantance kuɗaɗen harajin ‘stamp duties’ daga asusun ajiyar kuɗaɗe.
“Duk wanda ya san yadda Dokar Najeriya ta ke, ya san ta hana Ɗan Majalisa ya yi sakataren wani kwamiti mai mambobin gwamnatin tarayya a matsayin ‘yan kwamiti.
“Ban san inda ya shafto waɗannan kuɗaɗen da ya ambata har naira tiriliyan 89 ba. Domin ko jari da kadarorin bankunan ƙasar nan ma bai kai naira tiriliyan 50 ba..”
Garba Shehu ya ce Gudaji ai kowa ya san cewa mutumin Shugaban Ƙasa ne, babu mai iya hana shi ganin Buhari.
Discussion about this post