‘Yan Arewacin Najeriya ta fuskanci wasu al’amurori da muhimmai da suka auku a cikin shekarar 2022, wand aba za a taba mantawa da sub a a tarihin yankin da suka hada da harin da yan bindiga suka kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna da kuma gano danyen mai da aka yi a yankin Gombe da Bauchi.
1. Harin da ‘Yan Ta’adda suka kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna
‘Yan ta’adda sun rika cin karen ba babbaka a yankin Arewacin Najeriya a cikin shekarar 2022. Baya ga sace mutane da suka rika yi suna karbar kudaden fansa, ‘Yan Ta’adda a shekarar 2022 sun kaiwa wa jirgin kasan Abuja-Kaduna a cikin watan Maris. ‘Yan ta’addan sun saka nakiya a layin dogon. Bayan ta fashe jirgin kuma ya tsaya cak sai suka shiga cika suka kashe wasu sannan suka sace mutum akalla 60.
Da yawa daga cikin fasinjojin da aka tafi dasu sun shafe watanni tsare. Wasu da aka sako kuma kafin a sake su sai da aka rika biyan kudin fansa masu yawan gaske.
2. Yadda reshe ya juye da Tukur Mamu, mai yin sulhu da ‘yan Ta’adda
Tukur Mamu wanda shine mawallafin jaridar Desert Herald ya afka cikin tsaka mai wuya bayan an damke shi a kasar Masar a hanyar sa ta zuwa Saudi Arabiya tare da mai dakin sa . Jami’an tsaro na sirri (SSS) sun ce sun tsare Mamu ne domin ya amsa tambayoyi game da wasu abubuwa na sirri da ka samu a gidan sa. Mamu bai amsa laifi ba inda daga baya aka janye zarge-zargen da ake tuhumar sa akai.
3. Danyen Mai a Arewa
Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin fara haƙo ɗanyen mai a Kolmani, yankin da ke jihohin Bauchi da Gombe.
Wannan wani tarihi ne mai tabbatar da samun ɗanyen mai a Arewa, bayan shafe shekaru ana ta fafutikar aikin nema.
Cikin watan Oktoba, 2019 ne NNPL ta tabbatar da cewa an gano akwai ɗanyen mai da gas a ƙarƙashin ƙasar yankin Kolmani, kuma mai tarin yawan gaske.
Wurin wanda ke da faɗin gaske, ya shafi yankin Upper Benue Basin har zuwa Gongola Basin.
Kamfanin Sterling Global Oil, NNDC da NNPCL ne za su yi aikin haƙo ɗanyen man a Yankin Kolmani Oil and Gas Field.
Da ya ke ƙaddamar da fara haƙar ɗanyen man a Bauchi, Buhari ya ce aƙalla akwai ɗanyen mai a yankin fiye da ganga biliyan 1, kuma akwai gas zai kai cubic biliyan 500.
4. Nada Kasurgumin Dan Ta’adda sarauta a Zamfara
Masarautar ‘Yandoton Daji na ɗaya daga cikin sabbin masarautu biyu da Gwamnatin Zamfara ta ƙirƙiro cikin watan Mayu. An ciri masarautar daga Masarautar Tsafe. Aliyu Marafa ne aka naɗa Sarkin ‘Yandoton Daji.
An amince a naɗa wa gogarma Aleru sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoton Daji tsakanin su dattawan masarautar da kuma amincewar shi Aleru ɗin.
Wannan nadi da aka yi ya jawo cecekuce a tsakanin mutanenn Najeriya da ya kai ga saida gwamnatin jihar ta dakatar da baraken da ya nada Aleru sarauta a masarautar.
5. Ambaliyar Ruwa
A cikin wannan shekara an yi fama da ambaliyar ruwa a yankin Arewa. Jihohi kamar su Jigawa, Bauchi, Kano, Kaduna, Yobe da sauran yankuna da dama sun yi fama da matsalar ambaliya. An rasa rayuka masu yawan gaske sannan kuma dubban mutane sun rasa matsugunan su.
6. Kisar Deborah a Sokoto
A cikin wannan shekara an samu tashin hankali a Jihar Sokoto inda matasan makarantar koyon aikin malunta na Shehu Shagari dake Sokoto suka yi wa wata dalibar makaranta dukar mutuwa. An kashe Deborah ne kan wasu kalaman batanci da ta yi ga manzon Allah SAW.
Kafin hukuma su saka baki, an kashe ta. Hakan ya sa gwamnati ta rufe makarantar sannan kuma aka ja kunnen matasa kan saurin daukan doka a hannun su.
7. Rasuwa da aka yiyyi
A cikin shekarar 2022 yankin Arewa ta yi rashin wasu manyan mutane daga yankin, kama daga malamai, zuwa dattawan arziki da sarakai.
Cikin su akwai jikan marigayi Sardaunan Sokoto Hassan Danbaba, wanda ya rasu a watan Faburairu. Haka kuma a cikin watan Disamba da muke ciki Sarkin Sudan na Wurno, Abubakar Malami ya rasu.
Daga jihar Kano kuma akwai fitaccen dan siyasa Bashir Tofa, shima da Allah yayi wa rasuwa. Sannan kuma akwai babban Malami Sheikh Ahmad Bamba wanda shima ya rasu a cikin wannan shekara ne.
8. Tsige mataimakin gwamnan Zamfara
A cikin wannan shekara ne aka tsige mataimakin gwamna jihar Zamfara, Mahdi Ali Gusau. Majalisar jihar Zamfara ce ta tsige shi. Sai dai kuma tsigewar na da nasaba ne da kin sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC da yaki yi bayan gwamnan sa Bello Matwalle ya sauya sheka.
9. Badakalar Dan Sanda Abba Kyari
A cikin shekarar 2022 aka samu fitaccen dan sanda Abba Kyari da hannu dumu-dumu a harkarlar safarar muggan kwayoyi da suka hada da hodar Ibilis. Tuni aka mika shi ga hukumar NDLEA domin ci gaba da binciken sa. A cikin laifukan da ake tuhumar sa da su harda alaka da yake da shi da fitaccen dan yaurar nan HushPuppi da yanzu haka ke tsare a kurkukun Amurka.
10. Akanta Janar Ahmed Idris
Harkallar biliyoyin kudi da aka samu tsohon Akanta janar din Kasa Ahmed Idris na da hannu dumu-dumu a ciki. An zarge shi da handame sama da naira Biliyan 100 wanda ya dumbuza daga baitil malin gwamnatin tarayya.
11. Dambarwar Dangote da Yahaya Bello
A cikin wannan shekara ne hamshakin Attajiri Aliko Dangote ya saka kafar wando daya da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Yahaya Bello yayi barazanar kwace kamfanin Siminti na Obajana mallakin Dangote. Gwamnatin Kogi ta zargi Dangote da kauce wa biyan harajin jihar da kuma mallakan wannan wuri da ya gina kamfanin ba tare da an bi ka’ida ba.
12. Arangamar Malaman Kano, Ganduje da Sheikh Abduljabar Kabara
A cikin wannan shekara an yi ta kai ruwa rana da sheikh Abduljabbar Kabara a garin Kano, inda malamai suka zarge shi da yin batanci ga annabi SAW. An kai shi Kotu kuma a cikin Disamba kotun musulunci ta yanke mishi hukuncin kisa. Kafin a yanke wannan hukunci gwamnatin Kano ta dakatar dashi daga karatu sannan kuma ta rufe makarantun sa da masallacin sa.
Discussion about this post