• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

    KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

    ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

    Thugs-attack-collation

    ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

    2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

    ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Daga Ƙarfe 11 Zuwa 12:30 Na Ranar Zaɓe

    INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

HARE-HARE: Gaggauta hukunta masu kai wa INEC hari zai kawo ƙarshen lalata kayan zaɓe – Farfesa Yakubu

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
December 2, 2022
in Manyan Labarai
0
HARE-HARE: Gaggauta hukunta masu kai wa INEC hari zai kawo ƙarshen lalata kayan zaɓe – Farfesa Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukunta masu kai hare-hare da lalata dukiya da kayayyakin hukumar a faɗin ƙasar nan cikin hanzari ita ce hanyar da za a bi a magance matsalar.

Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin buɗe taron kwana biyu don buɗe idon Zaunannun Kwamishinonin Zaɓen hukumar (RECs) da aka yi a Legas a ranar Laraba.

Hukumar Cigaban Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ita ce ta ɗauki nauyin shirya taron.

A jawabin sa na buɗe taron, Yakubu ya bayyana cewa a cikin watanni huɗu da su ka gabata, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hare-hare a ofisoshin hukumar da ke ƙananan hukumomi biyar na ƙasar nan.

A cewar sa, muhimman kayayyaki da dukiyoyi sun salwanta a lokacin waɗannan hare-haren, don haka ya kamata a magance abin da ke faruwa a cikin gaggawa.

Ya ce: “Waɗannan kayayyakin sun haɗa da jimillar akwatunan zaɓe guda 1,992, da rumfunan zaɓe 399 da janaretocin ba da wuta guda 22, da kuma dubban katinan zaɓe da ba a kai ga karɓa ba, da wasu kayan.

“Tilas ne a dakatar da waɗannan hare-haren kuma a kai masu aikata su kotu. Aikin mu shi ne mu gudanar da zaɓe. Hanyar da ta fi dacewa domin magance matsalar ita ce a kama masu kai hare-haren a gurfanar da su a kotu.

“Babban maganin matsalar shi ne a kama ɓata-garin a hukunta su saboda ‘yan iska da masu ƙone-ƙone su daina tunanin cewa an amince da aikin assha a ƙasar mu. A gaskiya, abin baƙin ciki ne a ce ana yin wannan a lokacin da zaɓuɓɓuka ke ƙaratowa.

“Sai dai kuma, ina so in tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa za mu ga bayan waɗannan hare-haren, za a maye gurbin waɗannan kayan. To amma akwai iyakar yadda za mu iya ci gaba da maye gurbin kayayyakin da mu ka rasa a yayin da ya rage mana kwana 86 kacal kafin ranar babban zaɓe.”

A cewar sa, hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da dukkan mutanen kirki ‘yan Nijeriya domin hana hare-haren.

Ya ce INEC ta duƙufa wajen tabbatar da cewa babu abin da zai hana a gudanar da zaɓuɓɓuka kamar yadda aka tsara, “kuma muradin al’ummar Nijeriya zai cika. Wannan shi ne mu ke ƙara tabbatar wa da ‘yan Nijeriya.”

A game da taron buɗe idon, Yakubu ya ce wani ɓangare ne na shirye-shiryen da ake yi domin manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.

Ya ce: “Mu na yin taro ne da dukkan Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe domin mu na sane da cewa an rantsar da 19 daga cikin su kimanin mako huɗu da su ka gabata.

“Mun yi tunanin cewa ya kamata a shirya masu taron buɗe ido domin su fahimci hanyoyi da ƙa’idojin aiki saboda za a yi zaɓe nan da kwana 86.”

Shugaban na INEC ya ce taron buɗe idon zai kuma mai da hankali ga ainihin ƙa’idar aiki kan karɓar katittikan zaɓe, da ƙa’idojin rarraba masu zaɓe zuwa rumfunan zaɓe, da tsarin yadda ake raba kayan zaɓe, da dokokin ɗabi’u da halayyar membobi da jami’ai da ma’aikatan hukumar.

“Hukumar ba jam’iyyar siyasa ba ce. Hukumar ba ta da ‘yan takara a zaɓuɓɓukan da ke tafe.

“Dukkan jam’iyyun siyasa daidai su ke da juna a wajen hukumar. Zaɓi ya rage wa ‘yan Nijeriya, wato masu zaɓe.

“Aikin mu shi ne mu tabbatar da darajar ƙuri’u, ba daɗi ba ƙari.”

Da ya ke magana kan ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa wai mutum zai iya kaɗa ƙuri’a ba tare da katin zaɓe ba a ranar zaɓe, Yakubu ya bayyana wannan maganar da cewa “ko kaɗan ba gaskiya ba ce,” ya na cewa, “kafin kowane mutum ya yi zaɓe, sai ya kasance ya yi rajista a matsayin mai zaɓe, kuma an ba shi katin zaɓe.

“Tun tuni hukumar ta fito da dokar cewa ‘ba katin zaɓe, ba zaɓe’. Babu abin da ya canza. Dokar ce ta tanadar da hakan, saboda haka in aka yi wani abu daban to an karya dokar.

“Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan shaci-faɗin cewa wai mutum zai iya kaɗa ƙuri’a a ranar zaɓe ba tare da katin zaɓe ba.”

Da ya ke yaba wa UNDP saboda ɗaukar nauyin shirya taron da ta yi, Yakubu ya ce haɗin gwiwar da ta daɗe ta na yi da INEC ya jima kuma ya taimaka gaya wajen yauƙaƙa cigaban da ake samu a wajen harkokin shirya zaɓe.

A saƙon sa na fatan alheri, Mista Deryck Fritz, wanda shi ne babban mashawarcin UNDP, ya yi kira ga kwamishinonin da su dage sosai wajen aiwatar da tsare-tsaren hukumar kuma su kasance kan gaba wajen masu magance matsaloli idan sun taso.

Ya ce su ne za su sa ido kan aiwatar da dukkan ayyukan da su ka rataya a wuyan hukumar kamar yadda aka ba su amana.

“Ku ne waɗanda za su yi aiki da abokan hulɗa da ke yankunan ku da ƙungiyoyin ‘yan sa kai, da hukumomin jiha, da goyon bayan ƙungiyoyin sufuri, da sauran masu ayyuka, da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

“A wannan waƙati na gasar Kofin Duniya, ana tuna mana da cewa zaɓuɓɓuka masu nasara, kamar gasannin ƙwallon ƙwafa masu nasara, su na samuwa ne sakamakon haɗin kai tare da aiki tare.”

Ya ce irin waɗannan ƙalubale za su jarraba ƙarfin hanyoyi da dokokin INEC, har ma da sadaukarwar ma’aikatan ta.

Ya ce tsarin dimokiraɗiyya, a sassa da dama na duniya, ya na fuskantar barazana, ya ƙara da cewa samar da tsari mai ƙarfi ne zai yi maganin wannan barazanar.

“INEC a matsayin ta na hukumar da tsarin mulki ya ba alhaki, tilas ta kasance kuma a ga ta kasance ba ta nuna wariya a matsayin ta na alƙalin zaɓe.”

Dukkan Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe na INEC da manyan ma’aikatan hukumar sun halarci taron.

Tags: AbujaHausaINECNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Jihohi 36 sun karɓi Naira tiriliyan 6.5 cikin shekaru bakwai – Zainab, Ministar Kuɗi

Next Post

ALAMOMIN ƘARSHEN WA’ADIN MULKI: Gwamnatin Tarayya ta ce gwamnoni ne su ka ƙaƙaba wa jama’a talauci da ƙuncin rayuwa a Najeriya

Next Post
Ba za mu biye wa Farfagandar ‘yan ta’adda ba, mun san abinda muke yi kuma za mu gama – Buhari

ALAMOMIN ƘARSHEN WA'ADIN MULKI: Gwamnatin Tarayya ta ce gwamnoni ne su ka ƙaƙaba wa jama'a talauci da ƙuncin rayuwa a Najeriya

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Abubuwa 11 da ake so a yawaita yi a watan Ramadan
  • ZABEN KADUNA: PDP ta yi murdiya a wasu kananan hukumomi, zan Kalubalance su a Kotu – Uba Sani
  • SABUWAR ƁARAKA A PDP: An dakatar da Fayose, Anyim, Gwamna Ortom zai gurfana gaban kwamitin ladabtarwa
  • Yunƙurin ‘yan majalisar APC uku masu so a halasta tu’ammali da tabar wiwi ya samu cikas
  • ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Keyamo ya roƙi SSS su kama Obi da Datti, saboda furucin cewa ‘zaɓen 2023 daidai ya ke da mulkin soja’

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.