Gwamnatin Kogi ta soki hukumar EFCC da yi wa gwamna da gwamnatin jihar Bita-da-Ƙulli da tonon silili, don ta tozarta gwamnan jihar.
A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kinsley Fansho ya fitar ranar Juma’a ya ce hukumar na yi wa gwamnan jihar zagon kasa ne da kuma kokarin tozarta shi domin biyan bukatun wasu da ke iza su su yi wa jihar irin wannan cin mutuncin.
” Haka a baya hukumar ta buga cewa wai gwamnan jihar ya handame wasu kuɗaɗe har Naira biyiyan 29 amma a karshe kunya ta ji domin bincike ya nuna gwamnatin Kogi bata aikata harkalla irin haka ba.
Harkallar naira biliyan 10
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta danƙara Ali Bello da Dauda Sulaiman kurkuku, bisa tuhumar su da kamfatar kuɗaɗen baitilmalin Jihar Kogi, har Naira Biliyan 10.27.
Su Ali Bello, wanda ɗan’uwa ne ga Gwamna Yahaya Bello, ana tuhumar su ne da lodi da jigilar kuɗin su ka kai wa wani ɗan canji ko dai ya canja masu kuɗaɗen zuwa dala, ko kuma ya adana masu.
Baya ga Ali Bello da Dauda Sulaiman, na ukun su shi ne wani mai suna Abdulsalami Hudu, babban jami’in kuɗaɗe na Majalisar Kogi, wanda tuni ya cika wandon sa da iska, zakara ya ba shi sa’a, ya dafe ƙeya ya tsere.
Sun jidi kuɗaɗen tsakanin Janairu zuwa Disamba, 2021 a Abuja.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa sun aikata laifin satar kuɗin al’umma daga baitilmalin Jihar Kogi. Kuma laifin su ya saɓa wa Dokar Najeriya Sashe na 18 (c) da 15 (2) (d), Dokar Haramcin Harƙallar Kuɗaɗe ta 2011 da aka yi wa kwaskwarima.”
Su ukun dai ana tuhumar su ne da kimshe kuɗaɗen tare da Rabi’u Usman Tafada, ɗan canjin da aka kai wa canji ko ajiyar kuɗaɗen.
EFCC ce ta maka su kotu, amma dai sun ce ba su aikata laifin da ake tuhumar su da aikatawa ba.
Lauyan EFCC wanda ya gurfanar da su a kotu, mai suna Rotimi Oyedepo, ya roƙi kotu ta aza ranar da za a fara shari’ar.
Lauyan wanda ake tuhuma na biyu ya nemi a ba shi belin dukkan waɗanda ake hutuma ɗin, amma bai yi nasara ba.
Mai Shari’a Omotosho ya bayar da belin ɗan’uwan Yahaya Bello kan kuɗi Naira biliyan ɗaya, sannan kuma masu beli mutum biyu su kasance sun rubuta wa kotu amincewar maƙala masu kuɗin kandagarkin tsrewar wanda aka yi beli har Naira biliyan 2 kowanen su. Kuma tilas sai kowanen su ya na da kasar da ta kai Naira miliyan 500 a Abuja.
Masu karɓar beli su kasance sun kai takardun mallakar kadarorin su ga Rajista na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, kuma su kai takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku da su ka gabata.
Daga nan Mai Shari’a ya tura su Kurkukun Kuje, har zuwa ranar da za a samu waɗanda su ka cika tsauraran sharuɗɗan beli, sannan a sake su.
Za a ci gaba da sauraren shari’ar a ranar 6 Ga Fabrairu, 2023.