Gaggan ƴan siyasan jihar Zamfara da ba su ga maciji da juna sun yi sulhu, sun haɗa kai gaba ɗayan su domin tunkarar zaɓen 2023.
Sanata Kabiru Marafa, AbdulAziz Yari, Gwamna Bello Matawalle, Mansur Dan-Ali, Bashir Yuguda, da Hassan Sahabi.
Da yake jawabi a wurin taron siyasar, gwaman Bello Matawalle ya ce jihar Jamfar ta APC ce kuma ita kaɗai ake yi saboda haka kowa ya shiga tafiyar tunda wuri, wanda ya ce ba zai bi kuma ba ɗan asalin jihar bane.
” Duk wani jigo ɗan asalin Zamfara da ya ke gwaska kuma ya ce ba APC zai yi a jihar ba, ba dan asalin jihar Zamfara ba ne ya koma jihar Katsina da zama.
Dukkan mu a jihar Zamfara Tinubu ne ɗan takarar mu kuma shi za mu yi, daga sama har kasa APC za mu yi.
A na shi jawabin a wurin taron tsohon gwamna AbdulAziz Yari ya yi kira ga magoya bayan sa da APC kaf na jihar Zamfara su zaɓi Tinubu ne a zaɓe mai zuwa.
Idan ba a manta ba shi kan sa gwamna Matawalle kotu ce ta yi masa gwamna a jam’iyyar PDP, bayan ta kwace daga hannun APC ta baiwa wa PDP. Daga baya sai Matawalle ya canja sheka zuwa APC mai mulki.
Tun daga lokacin suke takun saka tsakanin sa da tsohon gwamna da wasu manyan APC bangare Yari.
Discussion about this post