Shugaba Muhammadu Buhari ya ragargaji yadda gwamnoni da ciyamomin ƙananan hukumomi ke ɗaure wa rashawa da cin hanci gindi, lamarin da ya ce su ne ke hana samar da ci-gaba a yankunan karkara.
Buhari ya yi wannan kakkausar suka a lokacin da ya ke jawabi wurin taron Manyan Jami’ai na 44 (2022), a Cibiyar Nazarin Tsare-tsaren Mulki, Kuru, a Abuja, ranar Alhamis.
Buhari ya bada labarin irin gaganiyar da ya sha wajen daƙile cin hanci da rashawa.
Ya bada labarin irin gaganiyar da ya riƙa sha da wasu gwamnoni dangane da yadda su ke riƙon ƙananan hukumomin su.
“Ina ganin ya zama dole na ɗan saki layi daga abin da na ke bayani a kai, tunda na gama jawabi na. Abin da zan bada labari kuwa, ni ganau ne, ba jiyau ba.
“Wato irin harƙallar da su ke yi, idan misali kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya za ta bai wa wata jiha naira miliyan 100 ne za a bai wa ƙaramar hukuma, sai jiha ta ba shi naira miliyan 50, amma zai sa hannu cewa naira miliyan 100 ya karɓa.
“Sauran Naira miliyan 50 kuwa sai gwamna ya sa aljihu, sai fa wanda ya ga dama zai bai wa ladar-ganin-ido.
“Shi kuma shugaban ƙaramar hukuma, sauran kuɗaɗe ko biyan albashi ba za su ishe shi ba. Daga nan sai ya yi watsi da ayyukan raya karkara, da ya biya kan sa da wasu manya ‘yan ƙalilan, sauran shi ma sai ya watsa cikin aljihun sa.
“To abin da ke faruwa kenan yanzu a Najeriya. Lamarin ya yi muni matuƙa. Kuma abin takaici, masu ilmi ne ke yin wannan ha’inci.” Inji Buhari.
Daga nan Buhari ya ja kunnen ma’aikatan gwamnati da sauran masu riƙa da muƙamai su riƙa aiki tsakani da Allah.