Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shawarci duk wanda ya san ya yi rajistar zaɓe, to ya gaggauta karɓar katin shaidar rajistar sa, domin babu wanda za a bari ya yi zaɓen 2023 ba tare da katin rajista ba.
Kwamishinan INEC na Jihar Katsina, Ibrahim Yahaya-Maƙarfi ne ya ƙara jaddada haka, a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, ranar Lahadi, a Katsina.
Ya ce hukumar zaɓe ba za ta bai wa wani uzirin yin zaɓe ba tare da katin shaidar rajista ba.
Ya ce INEC ta dakatar da ci gaba da rajistar masu zaɓe tun a ranar 31 ga Yuli, saboda tilas sai an ɗauki lokaci ana tattaunawa, tantancewa da kuma taskace bayanan masu rajistar, kafin a kai ga buga wa kowa katin rajista.
Maƙarfi ya ce ta wannan tsarin ne INEC ke wa masu zaɓe rajistar da za ta ba su damar zaɓen duk wani ko wata ‘yan takarar da su ke so su zaɓa.
“Sashe na 16(1) na Dokar Zaɓe ya wajibta wa INEC yi wa masu zaɓe rajista, buga katin rajista da kuma damƙa wa duk wanda ya yi rajista katin sa a hannu. Amma tilas sai wanda sunan sa ya fito a jerin sunayen da ke cikin rajista kaɗai za a iya bai wa katin zaɓe.
“Ya na da kyau a san cewa katin shaidar rajista shi ne shaidar amincewa mutum ya yi zaɓe, kamar yada Sashe na 47 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.
“Daga ranar 12 ga Disamba INEC za ta fara raba katin shaidar rajistar zaɓe, har zuwa ranar 22 ga Janairu, 2023.
“Za mu raba katin a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jiha, kuma za a koma ana rabawa a dukkan cibiyoyin rajistar zaɓe 361 na jiha daga ranar 6 zuwa 15 ga Janairu, 2023.”
INEC ta yi kira ga duk wanda ya san ya yi rajista ya je ya karɓi katin sa. Hukumar ta ƙara yin sanarwar cewa za a riƙa raba katin tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa 3 na yamma, a kullum har da ranakun Asabar da Lahadi.