Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke wa Doyin Okupe hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan kurkuku, saboda kama shi da aka yi da laifin harƙallar naira miliyan 702.
Da ta ke yanke hukunci a ranar Litinin ɗin nan, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta ce kotu ta kama Okupe da laifin karɓar zunzurutun kuɗi har naira milyan 702 daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Tsaro na lokacin, Goodluck Jonathan, wato Sambo Dasuƙi.
Okupe dai a lokacin shi ne Babban Mashawarcin Jonathan na Musamman a Harkokin Yaɗa Labarai.
Kotu ta ce laifin Okupe shi ne da ya karɓi kuɗin madarar su ya riƙa dola da jigila, maimakon a banki, kamar yadda Dokar Mu’amala da Adadin Kuɗaɗe a wajen banki ta tanadar, wato Sashe na 16 (1) da (2) na Dokar Haramcin Harƙallar Kuɗaɗe.
Da ta ke zartas da hukunci, Mai Shari’a Ijeoma ta sami Okupe da laifi a tuhuma ta 34 da ake yi masa.
A wannan tuhumar ce aka ɗaure shi shekaru biyu a kurkuku, ko kuma tarar naira 500,000.
Haka nan a tuhuma ta 35 zuwa ta 39, an yanke masa wasu shekarun biyu ko tarar naira 500,000.
Kotu ta ci gaba da tsare Okupe inda aka ba shi har wa’adin ƙarfe 4:30 na yammacin Litinin cewa idan bai biya tarar zuwa lokacin ba, to za a tasa ƙeyar sa zuwa kurkuku.
Discussion about this post