Kotun shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna ta tilasta Abubakar Shuaibu ya biya bashin Naira 180,000 din da ya karba daga wurin tsohuwar budurwarsa Fatima Ismail.
Ita dai Fatima ‘yar kasuwa ce kuma ta bayyana a kotun cewa ta bai wa Shuaibu Naira 230,000 domin ya gyara motar sa amma tun daga lokacin zuwa yanzu Naira 50,000 ne ya biya daga cikin kudin.
Ta ce ta matsaa wa Shuaibu ya biya ta sauran kudin amma ya ki biya.
Shuaibu ya tabbatar cewa ya karbi wadannan kudade daga hannun Fatima sai dai ya ce a lokacin da Fatima ta bashi kudaden ba ta fadi masa cewa a bashi ne ta bashi ba.
“A lokacin da muke tare Fatima ba ta son gani na cikin damuwa da ta ga rai na ya baci sai ta debi kudi ta bani.
“A dalilin haka ya sa a wannan rana ta bani wadannan kudade domin na gyara mota na.
Shuaibu ya ce a yanzu haka dai baya aiki amma ya yi alkawarin zai rika biyan Naira 20,000 duk wata.
Alkalin kotun Malam Abubakar Salihu -Tureta ya yanke hukuncin cewa Shu’aib zai rika biyan Naira 30,000 duk wata a mai makon Naira 20,000.
Salihu-Tureta ya ce Shuaib zai fara biyan kudin daga watan Janairu 2023.
Discussion about this post