Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin an dagargaje naira tiriliyan 89 na wasu kuɗaɗen harajin da aka daɗe ana tarawa.
A ranar Juma’a ce Ɗan Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure ya yi wannan zargi.
Sai dai kuma washegari a ranar Lahadi, Kakakin Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, ya ce wannan zargi na Gudaji Kazaure shafa-labari-shuni ne kawai, ba gaskiya ba ce.
Shehu ya ce ai dokar ƙasa ma ta haramta wani ɗan majalisar tarayya ya yi sakataren kwamitin da manyan jami’an gwamnati ke ciki.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, Kazaure ya ce shi ne Sakataren Kwamitin Gano Kuɗaɗen Harajin ‘Stamp Duties’, wanda kwamiti ne na Shugaban Ƙasa.
Kazaure ya ce CBN, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, sai kuma Manyan Hadiman Fadar Shugaban Ƙasa sun yi masa katanga, su ka hana shi ganin Shugaban Ƙasa, domin ya yi masa bayanin abin da binciken kwamitin sa ya gano.
Gudaji, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa, ya ce kwamitin sa ya zargi hukumomi da cibiyoyin gwamnati da laifin yi wa kwamitin sa zagon ƙasa.
Ya ƙara da cewa kwamitin sa ya bankaɗo cewa zunzurutun naira tiriliyan 89 ne aka karkatar, daga kuɗaɗen harajin da bankuna ke cirar wa gwamnati daga masu hulɗa da bankuna, wato stamp duties.
Sai dai kuma Garba Shehu ya maida masa martanin cewa ai tuni aka rushe kwamitin da shi Gudaji Kazaure ya ce shi ne sakataren kwamiti.
Sai dai kuma ya ce akwai kuma wani kwamiti wanda Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ke shugabanta, wanda aka kafa cikin Juni, 2020, wanda aikin kwamitin shi ne tantance kuɗaɗen harajin ‘stamp duties’ daga asusun ajiyar kuɗaɗe.
“Duk wanda ya san yadda Dokar Najeriya ta ke, ya san ta hana Ɗan Majalisa ya yi sakataren wani kwamiti mai mambobin gwamnatin tarayya a matsayin ‘yan kwamiti.
“Ban san inda ya shafto waɗannan kuɗaɗen da ya ambata har naira tiriliyan 89 ba. Domin ko jari da kadarorin bankunan ƙasar nan ma bai kai naira tiriliyan 50 ba..”
Garba Shehu ya ce Gudaji ai kowa ya san cewa mutumin Shugaban Ƙasa ne, babu mai iya hana shi ganin Shugaban Ƙasa.
Discussion about this post