Hukumar EFCC ta sanar da cewa a ranar 9 Ga Janairu za ta yi gwanjon wasu kadarorin da su ka haɗa da manyan gidaje, filaye da fulotan da ta ƙwato daga yawancin ɓarayin gwamnati da kuma mazambata.
Za a yi gwanjon kadarorin ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023, a dandalin taron yaye ɗalibai na Jami’ar NOUN da ke maƙwautaka da Hedikwatar EFCC.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Haka nan kuma EFCC ta umarci dukkan masu son shiga neman sayen kadarorin ya aika wa hukumar da buƙatar sa a rubuce nan da ranar Litinin, 9 Ga Janairu, 2023 sannan a bi nan efcc.gov.ng
Idan ba a manta na, Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa dai tun a ranar 16 Ga Disamba ya sanar cewa nan ba da daɗewa ba hukumar sa za ta fara sayar da kadarorin da ta ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati a, faɗin ƙasar nan.
Ya faɗi cewa za a koma sayar da kadarorin ne na gidaje, fulotai da filaye masu yawa bayan kammala sayar da motocin da aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda aka samu ‘yar tirja-tirja wajen taron gwanjon motocin da aka ƙwato daga ɓarayin Gwamnati.
Kantama-kantaman gidajen da za a sayar dai sun haɗa da wasu gidaje 61 masu tsadar kayan alatu da maka-makan filaye.
Akwai gidaje 24 a Tsibirin Banana da ke Legas, wasu gidajen alfarma 21 da ke Yaba, Legas, sai kuma wasu gidaje 16 a rukunin gidaje na Heritage Court Estate a Fatakwal.
Akwai wasu gidajen da filaye a Jihar Legas, wasu a Abuja da kewaye, akwai Anambra da Ebonyi da Gombe da Kaduna.
Sauran sun haɗa da gidaje dailaye a Delta, Edo , kantamemen otal da Plaza a Kwara, sai kuma gidaje da filaye a Cross Riba, Osun da Oyo.
Za a yi gwanjon a ranar 9 Ga Janairu, 2023 zuwa ranar Juma’a, 13 Ga Janairu, 2023.
Discussion about this post