Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa, ya tabbatar da cewa hukumar sa ta ƙwato naira biliyan 30, daga cikin naira bilyan 109 ɗin da ake zargin tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya sace.
Bawa ya sanar da manema labarai haka, lokacin ganawar sa da ‘yan jaridar Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Alhamis a Abuja, a Aso Rock Villa.
Bawa ya gabatar da bayanin a taron mako mako na da ma’aikatu ke yi da manema labarai, su na bayyana masu ayyukan da su ka gudanar.
Hadiman Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasa ne ke shirya tarukan, kuma wannan ne taro na 62 tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari mulki a cikin 2015.
Wannan shiri da aka gudanar a ranar Alhamis, an nuna shi kai-tsaye a YouTube.
“EFCC ta samu nasarar ƙwato Naira biliyan 30 daga hannun tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris, wanda yanzu haka wannan hukuma ta gurfanar da shi a Babbar Kotun Abuja.”
A kotu dai ana tuhumar Idris da laifuka 14, ciki har da ɗirka gagarimar sata da kuma cin amanar haƙƙin da aka damƙa masa na kula da dukiyar al’umma.
A ranar 23 Ga Yuli ne Mai Shari’a J.O Adeyemi Ajayi ya bayar da belin Idris.
Sai dai kuma Bawa bai yi ƙarin haske ba shin zunzurutun kuɗaɗe har Naira biliyan 30 ne aka ƙwato a hannun Idris, ko kuwa adadin ya haɗa har da maka-makan kadarorin da aka ƙwato daga hannun sa.
Discussion about this post