Yan sandan jihar Kaduna sun kama wani kasurgumin dan bindiga kuma dillalin harsasai a Zaria, jihar Kaduna.
Kakakin rundunar Mohammed Jalige ne ya bayyana wannan nasara da ‘yan sandan suka samu a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Jalige ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama mutumin ne bisa babur a unguwar Kwarkwaron Manu, dake yankin Basawa, Tudun Wadan Zaria.
” Yan sanda dake fatorol a unguwar Kwarkwaron Manu, Basawa ne suka kama shi. Ko da suka hango su bisa babur din da babu lamba a jiki sai suka tsaida su. Wanda aka goyo ya sauka ya arce kafin ‘yan sandan su ankare. Daga nan ne fa aka damke matukin.
” Bayan an gudanar da bincike sai aka gano cewa wannan matukin kasurgumin dan bindiga ne kuma dillalin saida wa ‘yan bindiga bindigogi da harsasai. An kama buhu lode da harsasai har sama da 300 da aka kirga su, sannan da bindiga kirar AK47 4,da layu da guraye.
Discussion about this post