Ɗan takarar kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya Mohammed Sani Abdullahi da aka fi sani da Dattijo ya birge kirstocin Kaduna.
Ranar Laraba, ɗan takaran ya kaddamar da raba wa Kiristocin Kaduna ta Tsakiya kyautan buhunan shinfafa domin bikin Kirsimeti.
Darektan Kamfen ɗin Dattijo, Ahmed Maiyaki wanda shine ya wakilce shi a wurin Kaddamar da rabon, ya ce ɗan takaran ya yi haka ne domin Kiristoci su sami sauki a lokacin kiristimeti.
Kananan hukumomin da za su amfana da wannan taimako sun haɗa da Birnin Gwari, Kaduna ta Kudu, Kaduna Ta Arewa, Igabi, Chikun da karamar hukumar Kajuru.
Discussion about this post