Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa CBN ya maida fiye da naira tiriliyan 1 banki, tun lokacin daga lokacin da ta yi sanarwar sauya wa naira sabon launi da kuma bayar da wa’adin daina karɓar kuɗaɗen da ke hannun jama’a kafin fara amfani da sabbin launi.
CBN dai ya ce daga cikin dalilan da su ka haifar da sauya launin kuɗaɗen, har da ƙarancin kuɗaɗe a bankuna, inda har ta kai akwai naira tiriliyan 2.73 a hannun jama’a, waɗanda an ƙi kai su bankuna domin a ajiye.
Ya ce a 2015, kuɗaɗen da ke hannun jama’a ba su wuce naira tiriliyan 1.46 ba, har zuwa Disamba 2015. Amma zuwa Satumba 2022 kuɗaɗen da ke hannun jama’a sun kai naira tiriliyan 3.23.
Daga cikin tiriliyan 3.23 ɗin kuwa, tiriliyan 2.73 duk ba a cikin bankuna ake hada-hada da su ba. Emefiele ya ce wannan kuwa abin damuwa ne matuƙar gaske, wanda ba zai yiwu a bari a ci gaba da haka ba.”
Da ya ke ganawa da manema labarai a Daura, bayan a gana da Shugaba Muhammadu Buhari, Emefiele ya ce zuwa yanzu CBN ta maida fiye da naira tiriliyan 1 a hannun ta, bankunan kasuwanci su ma sun riƙe kusan naira tiriliyan 1 su ma.
CBN Ya Fara Sakar Wa Bankuna Sabbin Kuɗaɗe – Emefiele
Emefiele ya shaida wa manema labarai cewa CBN ya fara sakar wa bankuna sabbin kuɗaɗe, su kuma bankunan sun fara rarraba sabbin kuɗaɗen zuwa rassan su.
“Mun yi shiri sosai, saboda daga ranar 15 Ga Disamba za fara raba sabbin kuɗaɗe. Amma sai Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar tun a ranar 26 Ga Nuwamba.
“Ina sanar da ku cewa bankuna sun ma fara karɓar sabbin kuɗaɗe sun fara raba su tun daga jiya Laraba. Haka za a ci gaba da yi, har zuwa ranar da za a daina amfani da tsoffin kuɗaɗe, a ranar 31 Ga Janairu, 2023.
Barkwancin Emefiele A Daura: ‘An Fara Amfani Da Kuɗaɗen Da Mu Ka Shafa Wa Bula’
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi ‘yan jarida barkwanci, a lokacin da ya ke masu ƙarin bayani dangane da sabbin kuɗaɗen da aka sauya wa launi.
Da ya ke cewa CBN ta fara raba wa bankuna kuɗaɗen, su kuma sun fara bai wa jama’a su, shi ma ya kira su “waɗanda aka shafa wa fenti”, kamar yadda ‘yan Najeriya ke yi masu barkwanci.
“Ni ma dai bari na ɗan yi barkwanci. A yanzu za a riƙa amfani da sabbin kuɗaɗen da aka shafa wa bula tare da tsoffin kuɗaɗen da ba su da bula. Amma daga ranar 31 Ga Janairu, 2023, waɗanda ba a shafa wa bula ba sun daina amfani kwata-kwata. Saboda haka duk wanda ke da kuɗaɗen da ba a shafa wa bula ba, to garzaya ya kai su banki kawai.”
Discussion about this post