Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya, Ado Doguwa ya yi karin haske game da wasu kalamai da yayi a Kano game da jam’iyyar sa ta APC da zaben 2023.
Doguwa ya bayyana a wurin taron APC cewa duk wanda bai zaɓi APC a jihar Kano ba, zai yaba wa aya zaƙi. Ko dai ka zaɓi APC a 2023 ko kuma jikin ka ya gaya maka.
Waɗannan kalamai da yayi ya jawo cecekuce a tsakanin mutane inda suke ganin barazana ce yake yi wanda zai iya tada husuma tsakanin jama’a.
Da yake tattaunawa da talabijin ɗin Channels, Doguwa ya ce abinda ya faɗi ba wai haka suke nufi kamar yadda ya faɗe su.
” Mu a siyasar Kano, muna da wasu irin kalamai da ƴan siyasa kan yi domin nuna gogewar su a iya yi wa mutane jawabi da tsorata su don neman kuri’a.
Wannan kalamai ne kowa na siyasa amma ba don wai eh lallai haka za ayi a aikace ba.
Doguwa ya ce ” Mu a jihar Kano muna yin irin wannan kalamai a lokacin siyasa. Kuma hakan ya samo asaline ba tun yanzu ba tun lokacin tsoffin ƴan siyasan Kano. Da haka suke neman jama’a da kuma barazana da tsorata abokan adawa.
” Amma ba wai muna yin su bane don wai da gaske hakan za ayi, duk barazana ce kawai da ruɗun siyasa amma ba wani abu bane.