Ba ta karan kan ‘yan Najeriya da ke ɗanɗana tsadar rayuwa da ƙuncin fatara da rashin tsaro ba, shi kan sa wanda ke mulkar su ɗin, wato Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce har ya ƙagara wa’adin sa ya ƙare, bayan 29 Ga Mayu 2023, ya fita daga Fadar Shugaban Ƙasa, ya koma gida haka nan.
In dai Buhari ya gaji da mulkin sa na tsawon shekaru takwas, to ko shakka babu talakawa ma sun gaji da mulkin. Mai sayen shinkafa da ɗan karen tsada, bayan ya zaɓi Buhari don ya samu sassaucin farashin abinci, ya ƙagara ya sauka. Mai sayen taliya naira 100 kafin Buhari, yanzu ya ke sayen ta N450, shi ma ya ƙagara Buhari ya sauka.
Mai sayen takin zamani N6000, yanzu ya ke saye sama da N20,000, shi ma ya gaji. Mai sayen litar fetur N80, amma ya zaɓi Buhari don ya samu rahusa, sai yanzu ya ke sayen ta N350, shi ma ya gaji.
Waɗanda ke hannun ‘yan bindiga, waɗanda ‘yan bindiga su ka kora daga gidaje da garuruwan su, waɗanda su ka raba da maƙudan kuɗaɗe su ka biya fansa da waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe wa iyalai da waɗanda aka ƙwace masu matayen su ko ‘ya’yan su mata duk sun ƙagara su ka wannan mulki ya zo ƙarshe.
Shin Buhari ne ya kamata ya ce ya ƙagara mulkin sa ya ƙare ya koma gida ya huta, ko kuwa Katsina, Zamfarawa, Kabawa, Sakkwatawa da sauran waɗanda ‘yan bindiga su ka kassara a zamanin mulkin sa?
Ai idan ɗan dako bai ce ya gaji ba, to mai kaya bazai ce ya gaji ba.
Ina batun wa alƙawurran tsaro, daƙile cin hanci da rashawa da bunƙasa tattalin arziki? An cika alƙawurran ko kuwa sun zama kawalwalniya ruwan faƙo?
Mulkin Buhari ya zo ƙarshen yayin da ya kinkimo ruɗanin sauya launin kuɗi da kuma taƙaita cirar kuɗaɗe daga asusun bankuna.
A daidai ƙarshen shekarar nan, watanni kaɗan kafin saukar sa, bashi ya yi wa ƙasar nan katutu, ta yadda ko kasafin kuɗin 2023 na naira tiriliyan 20.5, tatsuniya zai koma muddin Najeriya na ta ciwo bashi daga ƙasashen waje domin aiwatar da ayyukan da ta ce za ta aiwatar a kasafin ba.
Ko tsaro ko ilmi, ko cin hanci da rashawa ko tsadar rayuwa ko fannin kiwon lafiya. Idan akwai alƙawurran da aka cika, ba abu ba ne ɓoyayye. Saboda a kullum ana fama da waɗannan matsalolin.
Idan ka tsallaka kayan da ake shigowa da su daga waje, a yau sabulun ‘Crusader’ guda ɗaya naira 1,100.00 ya ke. Kafin a rantsar da Buhari kuwa Naira 220 kacal ake sayar da shi.
Yaƙi da cin hanci da rashawa da aka shafe shekaru 12 Buhari na alƙawarin idan aka zaɓe shi zai daƙile shi, an wayi gari irin yadda aka riƙa fallasa masu manyan jiga-jigan gwamnatin Buhari, irin su Akanta Janar Ahmed Idris, tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da kuma badaƙalar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele wadda Honorabul Gudaji Kazaure ke fallasawa, sun nuna bilumbituwar da ke cikin yaƙi da rashawar, ta fi tasirin da yaƙi da cin rashawar ya yi a ƙasar nan.
Discussion about this post