Babban kotu dake jihar Kano ta bayyana Mohammed Abacha a matsayin dan takaran gwamna na jami’yyar PDP a Kano.
Kafin haka hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana Aminu Wali dan tsohon ministan harkokin waje Sadiq Wali a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jami’yyar PDP.
Idan ba a manta ba Mohammed Abacha shine dan tsohon shugaban Kasa na mulkin soja Sani Abacha.
A zaben fidda gwani na jami’yyar PDP wanda da aka yi wani bangaren jami’yyar ta zabi Abacha ne a matsayin dan takaran ta dayan fannin ta zabi Wali.
Sai dai kuma hukumar Zabe ta kasa ta amince da Wali a matsayin dan takaran kafin wannan hukunci da kotu ta yanke.
Alkalin kotun Abdullahi Liman a ranar Alhamis ya yanke hukuncin cewa Abacha ne ya ci zaben fida gwanin jami’yyar PDP.
Kotun ta Kuma dakatar Wali da ya daina nuna kansa a matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano na jami’yyar PDP.
Liman ya kuma umarci hukumar zabe INEC ta musanya sunan Wali da Abacha saboda shine ya fi samun kuri’u a zaben fidda gwani na jami’yyar PDP da aka yi ranar 25 ga Mayu 2022.
Kuma hukumar Zabe da kanta ta halarci wurin zaben fidda gwanin da aka yi a garin Kano, saboda haka babu dalilin bayyana wani ba Abacha a matsayin dan takaran gwamnan jihar na PDP.
Discussion about this post