Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kanduna ya bayyana cewa har abada ba zai iya yin takarar zama ɗan majalisar dattawa a matsayin sanata ba, kamar yadda wasu gwamnoni ke yi bayan sun kammala wa’adin su na shekaru takwas kan mulki.
El-Rufai ya ce saurin hasala gare shi, saboda zuciyar sa ba ta iya jure kwatagwangwamar sa-in-sar da ake yi a Majalisar Dattawa.
Ya ce zama sanata sai jajirtacce, amma shi aikin gwamnatin da ya saba, shi ne wanda na sama ke bada umarni kuma tilas na ƙasa su bi. Sannan kuma na sama na da iznin ɗauka aiki ko tsigewa.
El-Rufai ya yi wannan bayani a wata lacca da ya yi dangane da aikin majalisa, wadda Cibiyar Nazari Majalisa da Dimokraɗiyya ta shirya, ranar Litinin a Abuja.
El-Rufai shi ne Shugaban taron.
“Majalisar Dattawa wuri ne da ni dai na san ba zan iya yin aiki a ciki ba, saboda ba ni da jimiri da juriyar yin haƙuri ana sa-in-sa da ni,” haka El-Rufai wanda ya taɓa yin ministan FCT Abuja ya bayyana.
“A Majalisar Dattawa dukkan Sanatocin daidai su ke, to kuwa babu shugabancin da ya fi aiki tare da mutanen da kai da a duk daidai ku ke. Shi ne aiki mafi wahala a ƙasar nan.
“Na san gwamnoni da dama idan sun kammala wa’adin su za su tafi Majalisar Dattawa.
“Amma ni ina tabbatar maku ba zan taɓa shiga zaɓe na zama sanata bayan na kammala gwamna ba.”
A yanzu dai akwai tsoffin gwamnoni 14 a Majalisar Dattawa.
Sannan kuma akwai gwamnoni takwas a yanzu waɗanda za su tsaya takarar sanata a zaɓen 2023.
Sun haɗa da Simon Lalong na Filato, Muhammad Badaru na Jigawa, Samuel Ortom na Benuwai, David Umahi na Ebonyi, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Darius Ishaku na Taraba, Aminu Tambuwal na Sokoto da Okezie Ikpeazu na Abiya.