Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sake jaddada cewa shi fa tun daga ranar da ya zama shugaban ƙasa a 2023 zai fara sauya wa Najeriya fasali.
Ya ce zai yi amfani da ajandar sa ta sauya fasalin Najeriya domin ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da fuskanta.
Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya ƙasa ta hanyar sake fasalin Najeriya.
“Babban muradin mu shi ne mu tabbatar mun kawar da dukkan matsalolin rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, kawar da danne haƙƙin tallalin arzikin ja’am’a da samar da aikin yi ga matasa. Ina ɗaukar maku alƙawarin cewa tun daga ranar da aka naɗa ni shugaba idan na yi nasara a zaɓen 2023, zan aiwatar da su,” inji Atiku.
Daga nan sai ya roƙi al’ummar jihar Osun su jefa masa ƙuri’un su, domin ya cimma burin sa na ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ya ce mulkin APC ya jefa ƙasar.
“Ba za mu kunyata ku ba, kuma ba za mu ci amanar ku kamar yadda APC ta ci amanar ku ba. Saboda mu na da ƙwarewa da irin gogewar da Najeriya ke matuƙar buƙata.”
Gwamna Ademola Adeleke, wanda aka rantsar kwanan nan, ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogagge kuma mai ƙwarewar da zai iya ceto Najeriya, har ya magance matsaloli da ƙalubalen da su ka dabaibaye ƙasar.