Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da fara kamfen ɗin sa na shiyyar Kudu maso Yamma a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Da ya ke jawabi a wurin gangamin da ya samu halartar ɗimbin magoya bayan PDP, Atiku ya ce Najeriya ta yi asarar shekaru takwas da APC ta yi ta na mulki, wanda su ka jefa jama’a cikin mawuyacin halin da ba shi kwatantuwa.
Ya yi fatan cewa, “daga 2023, kada Allah ya sake jarabtar ‘yan Najeriya da irin mulkin APC.”
Wazirin Adamawa ya yi alƙawarin farfaɗo da harkokin ilmi tare da inganta shi, ya na mai cewa “gwamnatin APC ta kashe harkar ilmi a ƙasar nan, ta hanyar bijiro da tsare-tsaren da kowa ya san ba su inganta ci gaban ilmi ba.”
Daga nan ya ƙara jaddada irin alƙawarin da ya yi a Ilorin, wanda ya ce idan ya yi nasara, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 domin bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu, ta yadda marasa za su yunƙuro wajen samun aikin yi sosai, su ma mata rayuwar su za ta ƙara bunƙasa.
Kafin ya fara jawabi, sai da uwargidan sa Titi Abubakar ta fara yi wa dandazon magoya bayan PDP jawabi tukunna.
Titi, wadda haifaffiyar Jihar Ondo ce, ta ce ta yi farin cikin ganin an PDP ta fara kamfen ɗin shiyyar Kudu Yamma a jihar ta ta haihuwa.
“Ina gabatar da kai na a gare ku, a matsayi na na ‘yar ku. Idan ku ka zaɓi miji na, zai daƙile Boko Haram kuma zai inganta ilmi.
“Kada ku manta, miji na ne ya yi nasara a zaɓen 2019, amma aka yi masa maguɗi, aka murɗe zaɓen. To kada ku bari a sake yaudarar ku. Wannan lokacin ma ku fito ku sake zaɓen PDP.
“Idan Atiku ya yi nasara, wata dama ce da Jihar Ondo za ta samu cewa ‘yar su za ta zama uwargidan shugaban ƙasa. Dama kuma Bayarabiya ba ta taɓa zama uwargidan shugaban ƙasa a Najeriya ba.”
Mataimakin takarar Atiku, Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce PDP za ta farfaɗo da fannin ilimi. Sannan ya nuna damuwar sa dangane da yadda ɗaliban jami’a su ka shafe watanni takwas a gida, ya na mai cewa ba za a samu irin haka a gwamnatin su ba.
Shi ma Gwamna Udom Emmanuel ya roƙi al’ummar Jihar Ondo su zaɓi Atiku, wanda ya ce shi kaɗai a cikin sauran ‘yan takarar zai iya haɗa kan Najeriya.
Shugaban jam’iyya Iyorchia Ayu da Babban Daraktan Kamfen, wato Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, duk sun yi wa taron jawabai masu nuna fifikon Atiku kan sauran ‘yan takara.