Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gargaɗi mazauna Legas cewa kada su sake tafka kuskuren sake komawa ƙarƙashin mulkin APC a tarayya da kuma jihar su.
Wazirin Adamawa ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin, a taron gangamin yaƙin neman zaɓen sa, wanda cincirindon jama’a su ka halarta a filin ƙwallo na Teslim Balogun, a Surulere.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku ya ce idan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa zai sauya fasalin Najeriya.
“Idan na yi nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023, zan sauya fasalin Najeriya. Shekara 23 kenan ku na zaɓen maigida ɗaya shi da iyalin sa. Yanzu lokaci ya yi da za ku ƙwatar wa kan ku ‘yancin siyasa. Ku tashi ku ɓalle dabaibayi da talalar da aka yi maku.
Atiku ya ragargaji mulkin APC a gangamin na Legas, daidai lokacin da shi kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ke Landan ya na taron bajekolin manufofi da ƙudororin sa a ɗakin taron Chatham House da ke Landan.
Atiku ya ƙaryata iƙirarin da APC ke yi cewa ta kawo ci gaba a Jihar Legas.
“Wane ci gaba aka kawo a Legas? An dai samu wani gida ɗaya tilo ya na mulkin Legas tsawon shekaru 23,” inji Atiku.
“Idan gwamnatin tarayya ta gina doguwar gasar Mainland, titin Agege da sauran tituna a jihar Legas. Ba gwamnatin jiha ta gina su ba.
“Lokaci ya yi da za ku ‘yantar da kan ku daga mulkin wani gida ɗaya tal na tsawon shekaru 23, ku zaɓi Jandor ya zama gwamnan Legas.”
Atiku ya yi alƙawarin sayar da dukkan matatun fetur na Kaduna, Warri, Fatakwal da Legas. Ya kuma ce zai ware dala biliyan 20 domin bunƙasa rayuwar mata da matasa.
“Mutane na ta tambayar yadda zan samu kuɗin da zan bunƙasa ƙasar nan har na inganta rayuwar mata da matasa. To idan na sayar da matatun mai na ƙasar nan, ta nan kuɗin za su fito hankali kwance,” haka ya shaida wa cincirindon magoya bayan PDP da su ka taru a wurin kamfen ɗin.
Tun da farko sai da ɗan takarar gwamnan Jihar Legas, Adeniran Abdul’aziz, wanda aka fi sani da Jandor, ya shaida wa magoya bayan PDP cewa zai hana cin zarafin da ‘yan gareji da ‘yan gada-gada ke wa jama’a a wurin shiga mota, musamman direbobi, kuma zai daƙile sauran ‘yan iskan da su ka addabi mazauna Legas.