Yanzu haka jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta gamu da cikas, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi a APC, Mohammed Abubakar ya bayyana goyon bayan sa ga Gwamna Bala Mohammed da ke sake takarar ci gaba da riƙe jihar a zango na biyu a ƙarƙashin PDP.
Wannan goyon baya da Abubakar ɗan adawa kuma ɗan APC ya nuna wa Gwamna Bala na PDP, ya haifar da ruɗani a cikin APC reshen Jihar Bauchi, har wasu daga cikin APC ɗin na tayar da ƙayar baya, su na kiran a kori Abubakar daga jam’iyyar kawai.
Mohammed Abubakar dai ya yi gwamna a jihar Bauchi daga 2015 zuwa 2019, amma a zaɓen 2019 bai yi tazarce ba, saboda Bala na PDP ne ya kayar da shi.
A lokacin zaɓen 2019, Mohammed Abubakar ya haƙƙaƙe cewa ‘yan cikin jam’iyyar sa, wato APC su ka kayar da shi su ka zaɓi Bala Mohammed, wato aka yi masa anti-party kenan.
PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa tsohon Gwamna Abubakar ya nuna goyon bayan sa ga Gwamna Bala, a lokacin walimar taya shi murnar zama Babban Lauya (SAN), wadda Gwamna Bala ya shirya masa a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.
Abin da ya fi harzuƙa shugabannin APC na Bauchi, shi ne ƙin halartar walimar da ɗan takarar gwamna na APC ta na jihar, Saddique Abubakar ya shirya wa Abubakar ɗin domin taya shi murna.
A janwabin sa, Abubakar ya bayyana cewa ya na irin karimcin da Gwamna Bala Mohammed ya nuna masa, kuma ya shirya masa.
Abubakar ya ce shi ma a baya ya shirya wa Bala irin wannan karramawa a Abuja, kuma ya yi mamaki da ya halarta.
“To haka ake so siyasa ta kasance, ba da gaba ba. Jiya APC ke mulkin Bauchi, yau kuma PDP. Kuma wanda ke PDP a yau, ana iya wayewar gari gobe da safe ya tsinci kan sa a APC, inji Abubakar, lokacin da ya ke santin walimar da Gwamna Bala ya shirya masa.
Sannan kuma ya jinjina wa Bala dangane da abin da ya kira, “gagarimin ayyukan ci gaban da ya samar wa jihar Bauchi.”
Abubakar Ya Watsa Mana Ƙasa A Ido – Barau, Kakakin Kamfen Ɗin Ɗan Takarar Gwamna A APC:
Barau ya bayyana rashin jin daɗin yadda Mohammed Abubakar ya halarci walimar da Gwamna Bala ya shirya masa a Bauchi, amma kuma ya ce ba zai halarci wadda Saddique Abubakar, ɗan takarar APC ya shirya masa a Abuja ba.
Ya ce Abubakar ya nemi a soke walimar ana saura kwanaki biyu kacal kafin ranar walimar.
“Kum kama hanyar ƙaton ɗakin taro, mun buga katin tsare-tsaren walima, mun sayi kayayyakin da su ka kamata, duk mun tanada. Amma ana saura kwana ɗaya sai ya kira ɗan takarar mataimakin gwamna ya ce ba zai halarta ba, don haka a fasa kawai.
Tuni dai har Nuhu Shugaban Matasan APC na jihar ya nemi a binciki lamarin, wasu kuma na kira da a gaggauta korar tsohon gwamnan daga APC.
Discussion about this post