Gwamnatin Tarayya za ta kaɗa wa kamfanin samar da wutar lantarki biyar ƙararrawar neman masu saye kuɗi hannu, domin samun kuɗaɗen da za a yi ayyukan kasafin 2023 da su.
Jaridar Blooberg ta ruwaito Babban Daraktan Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, Alex Okoh ya shaida wa Blooberg cewa za a zuba kuɗaɗen ne wajen ayyukan kasafin 2023.
Ya ce za a buga tandar neman masu saye tun daga cikin Disamba ɗin nan, kuma za a bar ƙofar neman waɗanda su ka fi saura farashi mai kyau, daga nan har ƙarshen watan Maris sannan a rufe.
Kasafin 2023 dai ya jefa Najeriya cikin tsomomuwa, ganin yadda Gwamnatin Buhari ta yi kasafin naira tiriliyan 20.5, amma kuma kusan rabi duk bashi ne za a ciwo.
Sannan kuma a cikin 2023 ɗin Najeriya za ta biya bashin sama da naira tiriliyan 6 ala tilas.
Tashoshin lantankin da za a kaɗa wa ƙararrawar sun haɗa da Tashar Samar da Wuta ta Geregu, Tashar Samar da Wuta ta Olorunsogo da sauran su.
Tuni dai ƙasashe da manyan bankunan duniya su ka fara ja baya daga bai wa Najeriya bashi.
Matsalar wutar lantarki a ƙasar nan sai ƙara muni ta ke yi, ta yadda a ƙasa mai al’umma kimanin miliyan 200, amma wutar da ta ke samu ba ta wuce migawat 4,000 kacal ba.
Alƙawurra da yawa wannan gwamnatin ba za ta iya cika su ba, ciki har da aikin titin jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
Discussion about this post