Shugaban kwamitin Kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar PDP, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya sanar da naɗin tsohon kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara a matsayy mamba a kwamitin.
Idan ba a manta ba, Dogara yayi hannun riga da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, David Babachir da shi ya sanar cewa Peter Obi zai bi.
Bayan Babachir ya sanar cewa da shi da Kiristocin Arewa kaf za su bi Peter Obi na Jam’iyyar LP, sai Dogara da wasu dake tare a cikin kungiyar adawar Muslim Muslim, suka barranta da wannan matsaya na Babachir, suka ce su Atiku za su yi.
Tambuwal ya ce ” Kwamitin Atiku ta saka Dogara a ciki.
Sai dai kuma sanin kowa ne cewa Dogara ya koma APC daga PDP ba a cikin shekarar 2021. Sannan bai sanar da sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba. Sai dai kuma gashi yanzu ya tsunduma cikin kwamitin kamfen din Atiku,
Dogara da nakarraban sa sunnlashi takobin ganin To nubu da jam’iyyar APC ba su yi nasara ba a zaɓe mai zuwa sabo tsaida musulmi da yayi mataimakin shugaban kasa.
Dogara ya ce gaba daya kiristocin Arewa ba za suyi jam’iyyar APC ba saboda musulmai biyu da suka tsayar ƴan takara.
Sai dai kuma an samu rarrabuwa a tafiyar bayan Dogara da makarrabannsa sun ɓalle daga tafiyar Babachir.
Discussion about this post