Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu, ya ƙaryata raɗe-raɗin da wasu ke yi cewa Amirka ta hana ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu bizar iznin shiga ƙasar ta.
Kalu ya fito a shafin sa na Facebook, ya wallafa cewa, Tinubu ya ɗaga tafiyar ce don ƙashin kan sa, amma babu wanda ya hana shi shiga Amurka.
“Tinubu zai bar Najeriya a ranar 4 Ga Disamba, inda zai dira Landan. A can zai gana da jama’a a katafaren ɗakin taron Chatham House,” inji Rundunar Kamfen ɗin TInubu.
Ta ce a Landan zai yi jawabi a Chatham House, inda zai gabatar da ƙudirorin sa, waɗanda za a tattauna su a wurin.
Ita ma cibiyar ta Chatham House ta tabbatar cewa Tinubu zai je ya yi jawabi a ranar 5 ga Disamba, inda zai gabatar da manufofi da ƙudirorin sa.
Tun da aka fara zaman muhawara da ‘yan takara, har yau Tinubu bai halarci gayyata ko ɗaya a ƙasar nan ba. Wasu na mamakin yadda zai ƙi halartar muhawarar nan cikin gida, amma kuma zai lula Amurka da wasu ƙasashen Turai.