Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari ta janye karar da ta shigar akan ɗalibi Aminu Mohammed, matashi dake jami’ar gwamnatin Tarayya dake Dutse.
Idan ba a manta ba Aisah ta sa a kama sannan a tsare dalibin bayan ikirarin da ta yi cewa ya ci mutuncin ta bisa wani rubutu da yayi a shafin sa ta tiwita.
Bayan sawa da tayi a kamo mata shi, ta sa an zane shi sannan ita ma da kanta an ce ta gaggaura masa mari, kamar yadda rahotanni suka nuna waɗanda aka saka a shafukan yanar gizo.
Sai dai kuma tun bayan kama wannan ɗalibi, ƴan Najeriya suka rika yin tir da abin da Aisha ta yi a matsayinta na uwar ƴan Najeriya.
Duk da cewa ba ya saurari kowa duk da kiraye kirayen da ak rika yi mata, a cikin wannan maka an aika da Aminu gidan yarin Suleja, sannan bayan haka kotu ta dage karar zuwa 30 ga watan Janairu.
Da yake janye karar da ake tuhumar wanda ake tuhumar a ranar Juma’a, lauyan masu shigar da kara, Fidelis Ogbobe, ya ce uwargidan shugaban kasa a matsayinta na uwar ƴan kasa ta yanke shawarar janye karar, biyo bayan tsoma bakin ‘yan Najeriya masu faɗa aji.
Da yake yanke hukunci kan lamarin, Mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ya jinjina wa Aisha Buhari bisa wannan namijin kokari da ta yi na janye karar.
Sannan kuma yayi kira ga iyaye su rika jan kunnen yayan su saboda gaba.