Babban Bankin Najeriya (CBN), ya amince da ƙara adadin kuɗin da za a riƙa cira a ATM da POS, daga naira 20,000 da ya bayyana da farko, inda yanzu ya amince a riƙa cirar naira 100,000 a kullum, naira 500,000 a cikin sati ɗaya.
Wannan ƙarin adadin dai ya zo ne bayan da Majalisar Tarayya ta umarci CBN ya ƙara yawan kuɗaɗen da za a riƙa cirewa a kullum, saboda ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi.
A yanzu dai CBN ya fitar da sabuwar sanarwar da ke ɗauke da umarni ga dukkan bankunan Najeriya. Sanarwar wadda ke ɗauke da sa hannun Daraktan Sa-ido Kan Harkokin Bankuna, Haruna Mustafa, ta ce CBN ya amince mutum ɗaya ya cire naira 500,000 a sati ɗaya, kamfanoni ko ƙungiyoyi kuma adadin naira miliyan 5 za su iya cirewa.
Yan Najeriya da dama su na ta korafe-ƙorafen rashin amincewa, har ta kai ga Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa su ka umarci Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya dakatar da shirin, kuma ta gayyace shi domin yi masa tambayoyi, amma bai amsa gayyatar ba.
A gefe ɗaya kuma fitaccen lauya Femi Falana ya ce wannan sabon tsari na CBN haramtacce ne, domin hakan ba zai yiwu ba har sai an maida shi ya zama doka tukunna.
Makonni biyu da su ka gabata dai Gwamnan CBN ya ce za a ɗan ƙara adadi, amma ba za a fasa aiwatar da tsarin ba.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce za a ɗan ƙara adadi, amma ba za a fasa aiwatarwa da tsarin taƙaita adadin kuɗaɗe daga hannun jama’a ba.
Ya ce tsarin na taƙaita adadin kuɗaɗen da mutane za su riƙa cira a ATM, POS da bankuna ya nan, amma dai za a ɗan sassauta, ta yadda za a iya yin ƙari daga naira 20,000 a kullum, N100,000 a sati da kuma Naira 100,000 da Naira 500,000 a bankuna.
Emefiele ya yi wannan bayani a ranar Juma’a, bayan ganawar sa Shugaba Muhammadu Buhari a Daura, inda shugaban ke hutun ƙarshen shekara a garin su.
Ya yi wannan bayani bayan da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa su ka gayyace shi cewa ya bayyana a gaban su a ranar Alhamis.
Sannan kuma Majalisar Wakilai ɗin ta umarce shi ya dakatar da duk wani shirin taƙaita adadin kuɗaɗen naira da za a iya cirewa a kullum.
CBN dai ta ce sabon tsarin cirar kuɗaɗen zai fara aiki ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023.
“Ina sane da gayyatar da Majalisar Tarayya ta yi min. Zan je, kuma zan yi masu bayani. Shi wannan tsari na taƙaita adadin kuɗaɗen da ke hannun jama’a, ai tun cikin 2012 aka fara shi.
“Amma kusan sau uku ko sau huɗu mu na so mu taƙaita kuɗaɗen da ke hannun jama’a, amma sai mu jingine tsarin, saboda mu na son ganin mun ƙara shiri sosai na sauƙaƙa hada-hada ta zamani a Najeriya.
“Shekaru 10 kenan tsakanin 2012 zuwa 2022. To a yanzu mun tabbatar cewa tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta kafofin zamani ya samu karɓuwa, kuma ya wadata sosai a faɗin ƙasar nan.”
Ya ce ana ci gaba da samar da hanyoyin sauƙaƙa wa mutanen karkara bin tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta zamani, musamman tu’ammali da POS, ta yadda tsarin bai kawo masu tawaya wajen hada-hada ko rayuwar su ɗungurugum ba.
“Yayin da na ke fitowa daga Daura yau ɗin nan, ai na ga wani shago mai ejan na POS.
“Akwai ejan na POS ɗin mu har miliyan 1.4 a faɗin ƙasar nan. Akwai su a ƙananan hukumomi da ƙauyuka da lungunan cikin karkara.”
Ya ce ejan na POS miliyan 1.4 kuwa ai tamkar ƙarin bankuna ne miliyan 1.4 a cikin ƙasa.
“Ba fa za mu zura idanu mu ƙyale fiye da kashi 85 cikin 100 na Naira su na watangaririya a wajen bankuna ba. Ƙasashe da dama a yanzu an daina hada-hadar jidar kuɗaɗe niƙi-niƙi, sai dai tsarin zamani ake bi.” Inji shi.
“Za mu sake nazarin adadin kuɗaɗen da za a riƙa cirewa. Amma ba za mu ƙara lokaci ko mu fasa tsarin ba,” inji Emefiele.
Discussion about this post