Ministan sufuri Mu’azu Sambo ya bayyana wa manema labarai cewa zirga-zirgar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki gadan-gadan cikin wannan wata da muke ciki ta Nuwamba.
Sambo ya kara da cewa gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin kada abinda ya auku a baya su sake faruwa.
Idan ba a manta ba, ‘yan ta’adda sun kai wa jirgin kasan hari a cikin watan Maris din wannan shekara inda suka kashe wasu fasinjoji sannan suka arce da wasu da dama.
A cikin watan Oktoba ne suka saki sauran fasinjoji 23 da ke tsare a hannun su.
Kafin wannan lokaci, ministan sufuri, Sambo ya yi alkawarin jirgin ba zai soma aiki ba sai an saki duka wadanda ke tsare hannun ‘yan bindigan da hakan ya sa sai yanzu ne za a dawo da aikin jigilar fasinjoji a wannan jirgi.
” ba ya ga addu’o’i da muke yi gwamnati ta saka matakan tsaro masu tsauri domin samar da tsaro ga fasinjoji.
Tun bayan daina aiki da jirgin yayi kasuwanci da harkallar mutane masu tuka motocin haya ya tsaya cak a tasoshin shirgin.
Wasu da dama sun koka kan wahalhalu da suka afka ciki na rashin kudi saboda rashin aikin jirgin.
Wannan dawowa da Jirgin kasa yayi ya farnta wa matafiya da dama rai ganin yadda babban titin Kaduna-Abuja ya yi mummunar lalacewa da bashi misaltuwa.
Discussion about this post